Harin kurkukun Kuje: Ido rufe 'yan ta'adda suka dinga neman inda Abba Kyari yake
- Wasu 'yan ta'addan da suka kai hari gami da kubutar da sama da 'yan gidan yarin Kuje 600 a daren Talata, sun nemi DCP Abba Kyari ruwa a jallo
- Wata majiyar sirri ta tabbatar da yadda hatsabiban bayan kubutar da 'yan Boko Haram 64 suka bazama daki-daki neman hazikin jami'in tsaron amma da kyar suka gan shi
- Yayin da suka gano an canza masa daki gami da tabbatar da tsaron da ba za su iya fasa wurin ba, hakan yasa 'yan ta'addan suka ranta a na kare
FCT, Abuja - Wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne sun kai farmaki gami da kubutar da sama da 'yan gidan yarin Kuje 600 a daren Talata, tare da neman inda DCP Abba Kyari yake amma basu samu nasarar fasa bangon bangaren gidan yarin da yake tsare ba.
Wata majiyar sirri ta bayyana yadda bayan tabbatar da an saki 'yan Boko Haram 64, tawagar 'yan ta'addan suka bazama bincikar daki-dakin wadanda suka zabi zama tare da tambayar inda Abba Kyari yake, ina Abba Kyari?
Yayin da suka samu labarin inda hazikin jami'in tsaron yake, sun garzaya wajen amma a rashin sanin su, an kara masa tsaro na musamman gami da canza masa daki kusa da kofar shiga wanda 'yan ta'addan ba zasu iya shiga ba, Vanguard ta ruwaito.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bayan sun yi yunkuri amma basu ga alamar nasara ba, 'yan ta'addan suka ranta a na kare.
An sake cafke 'yan gidan yari 100 da suka arce daga kurkukun Kuje
A wani labari na daban, kusan 'yan gidan yari 100 ne da suka arce daga matsakaiciyar gidan gyaran hali ta Kuje dake babban birnin tarayya a Abuja aka sake kamawa, jaridar Punch ta ruwaito hakan.
Kamar yadda ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya ya sanar, 'yan ta'addan Boko haram ne suka kai farmki gidan yarin inda suka saki mutum 600 ciki har da 'yan Boko Haram 64 dake tsare.
Jarida Punch ta ruwaito cewa, an cafke mutum 300 daga cikin wadanda suka tsere kuma ana kokarin damko sauran a dawo da su.
Asali: Legit.ng