Yanzu-Yanzu: Buhari Zai Shilla Senegal Yayin Da Ake Kai Hare-Hare Da Dama a Najeriya
- Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi birnin Dakar a Kasar Senegal don hallartar taron kungiyar cigaban kasa da kasa ta Afirka, IDA
- Babban mashawarcin shugaban kasa na musamman a bangaren watsa labarai Malam Garba Shehu ya ne bayyana hakan a ranar Laraba
- Sanarwar da ya fitar ta ce sauran shugabannin kasashen Afirka za su hallarci taron na IDA da ake fatan za a tattaunawa abubuwa da za su inganta tattalin arziki
Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Abuja a ranar Laraba, 6 ga watan Yuli domin hallartar kungiyar cigaban kasa da kasa, IDA, ta Afirka a Dakar, Senegal, rahoton Daily Trust.
Shugaban kasar zai yi tafiyar ne a lokacin da aka kai hare-hare da dama a kasar cikin awanni 24 da suka shude.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yan bindiga sun bude wa tawagar Shugaba Muhammadu Buhari a Katsina a ranar Talata.
Tawagar na hanyarta na zuwa Daura ne, garin shugaban kasa a lokacin da yan bindigan suka musu kwantar bauna.
A wani harin a Katsina, an bindige wani mataimakin kwamishinan yan sanda.
Kazalika, yan bindiga sun kutsa gidan yari na Kuje a Abuja, sun saki fursunoni har da manyan wanda ake zargin yan Boko Haram ne.
Ministan Tsaro, Bashir Magashi, ya ce dukkan wadanda ake zargin yan Boko Haram ne da aka tsare sun gudu yayin harin.
Wadanda za su yi wa Buhari rakiya
Cikin sanarwar da ya fitar ranar Laraba, kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya lissafa ministocin da za su yi wa Buhari rakiya; Ministan Harkokin Kasar Waje, Geoffery Onyeama; Ministan Kudi da Kasafi da Tsarin Kasa, Zainab Ahmed; da Ministan Masana'antu, Cinikayya da Saka Hannun Jari, Adeniyi Adebayo.
Shugaban kasa a 2023: Bana son tsohon hannu ya zama mataimakina, na fi son matashi mai jini a jika, Peter Obi
Sauran masu rakiyan sun hada da: Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele; Shugaban NIA, Amb. Rufai Abubakar; Shugaban Ofishin Kula Da Bashi, Patience Oniha; da Shugaban Bankin Masana'antu, Olukayode Pitan.
A cewar Shehu, Shugaban Senegal Macky Sall ne mai masaukin baki a taron da za a yi ranar Alhamis 7 ga watan Yuli kuma wasu shugabannin Afirka za su hallarci taron a Dakar.
Kakakin shugaban kasar ya ce ana sa ran abubuwan da za a tattauna za su taimaka wurin inganta tattalin arzikin kasashen tare da hadin gwiwa da Bankin Duniya/IDA.
Bayan Dawowa Daga Kigali, Buhari Zai Kai Ziyarar Aiki Portugal, Za A Karrama Shi Da Lambar Girma
A wani rahoton, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a yau, 28 ga watan Yuni, zai bar Abuja ziyarar aiki zuwa Portugal bayan gayyatar da Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa yai masa.
Garba Shehu, kakakin shugaba Buhari ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter inda ya ce Shugaba Buhari zai tattauna da takwararsa na Portugal, kuma za a karrama shi da lambar yabo na kasar ta ‘Great Collar of the Order of Prince Henry.’
Ya ce ana sa ran shugabannin biyu za su tattauna kan wasu batutuwa da ya shafi kasashen biyu kuma za a rattaba hannu kan yarjejeniya da ta shafi iyakokin kasa.
Asali: Legit.ng