Da duminsa: 'Yan daba sun kai wa 'yan majalisa hari, sun raunata mutum 6, sun ragargaza motoci
- 'Yan daba da suka kai wurin 50 sun kai wa 'yan majalisar jihar Bauchi farmaki a ranar Litinin yayin da suke tsaka da taro a kusa da gidan gwamnatin jihar
- Kamar yadda aka gano, harin da yayi sanadin jigatar mutum shida tare da lalacewar motoci, ya faru ne wurin karfe hudu na yammacin Litinin
- Lamarin nan ya faru ne bayan sa'o'i kadan da wasu mutane suka yi yunkurin kone majalisar jihar Bauchi wanda jami'an tsaro suka dakile
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Bauchi - Rikicin da ya rincabe a majalisar jihar Bauchi ya sake tsananta a ranar Litinin yayin da 'yan daba suka kai farmaki kan 'yan majalisar jihar.
'Yan daban da zasu kai 50 sun tsinkayi wani gidan saukar baki dake kan titin Sir Kashim Ibrahim, mitoci kadan tsakani da gidan gwamnatin jihar Bauchi kuma suka kai farmaki kan 'yan majalisar da suke taro a wurin.
'Yan daban sun raunata mutum shida, sun ragargaza motoci da tagogin gidan inda suka birkita komai na gidan tare da hargitsa shi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, mummunan lamarin ya auku ne wurin karfe 4 na yammacin ranar Litinin yayin da 'yan majalisar ke tsaka da taronsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan sa'o'i kadan da wasu da ba a san ko su waye ba suka yi yunkurin kone majalisar jihar Bauchi amma jami'an tsaro da suka yi martanin gaggawa suka hana su.
Bayan aukuwar lamarin, tawagar hadin guiwa ta jami'an tsaro da suka hada da 'yan sanda, NSCDC, DSS da sojojin Najeriya sun mamaye ginin majalisar.
A yayin rubuta wannan rahoton, jami'an tsari ne ke gadin ginin majalisar domin gujewa barkewar tarzoma.
Daya daga cikin 'yan majlisar da aka kai wa hari mai suna Ado Wakili, mai wakiltar mazabar Burra ta karamar hukumar Ningi, ya zargi cewa 'yan daban na dauke da bindigogi da sauran miyagun makamai.
"Muna tsaka da taron kawai muka ji hayaniya a waje tare da buga get. A lokacin da muka gaggauta zuwa mu ga me ke faruwa, 'yan daban sun shigo rike da bindigogi, adduna da sauran miyagun makamai.
“Dukkanmu mun watse domin neman wurin buya, da yawa daga cikinmu har da ni mun samu raunika kamar yadda kuke gani a fuskata kasa da idanuna.
"Sun birkita komai. A lokacin da muka fito, sun farfasa mana motoci da tagogin gidan," Wakili ya bada labari.
Tsohon kakakin majalisar jihar, Kawuwa Shehu-Damina, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin yace babu dalilin wannan tarzomar.
Asali: Legit.ng