Kar ku bari yan siyasa su yaudare ku da kyautar kuɗi, Don ga Malaman Addini

Kar ku bari yan siyasa su yaudare ku da kyautar kuɗi, Don ga Malaman Addini

  • Wani babban Malamin Jami'a, Farfesa Azeez Taofiq, ya roki Malaman addinin musulunci kada su ruɗu da kuɗin yan siyasa
  • A wani taron horar da Malamai, Taofiq ya ce rashawa ita ce tushen duk wata matsala, har rashin tsaro ya samo asali ne daga rashawa
  • Taron wanda ya gudana a Sokoto, gidauniyar Alhabibiyya ta shirya shi tare da taimakon gidauniyar MacArthur

Sokoto - An roki malaman Addinin Musulunci a Najeriya ka da su ruɗu da kyautar kuɗin da zata zo musu daga shugabannin siyasa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wani fitaccen malamin Jami'a, Farfesa Azeez Taofiq, shi ne ya yi wannan rokon ga Malaman Musulinci a wurin taron horar wa na kwana ɗaya da aka shirya wa shugabannin Addini a Sakkwato.

Kara karanta wannan

Duk Daya ne: Kiristoci sun taya Musulmai share Masallacin Sallar Idi a Kaduna

Farfesa Azeez Taofiq.
Kar ku bari yan siyasa su yaudare ku da kyautar kuɗi, Don ga Malaman Addini Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gidauniyar Alhabibiyya tare da tallafin gidauniyar MacArthur ne suka shirya taron horar wa na musamman ga shuwagabannin.

Cin hanci ne tushen sheɗanci - Taofiq

A cewar Farfesa Taofiq, cin hanci da rashawa ne asalin duk wani sheɗanci, inda ya ƙara da cewa rashin tsaron da ake fama da shi a sassan Najeriya ya samo asali ne daga cin hanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabansa ya ce:

"Mun zo nan ne mu faɗa wa Malaman mu cewa su yi amfani da harshen su wajen yaƙar cin hanci da rashawa, kar su shagala a janye musu hankali da ɗan abinda suke samu daga yan siyasa. Ku karɓa kuma ku faɗi gaskiya."
"Saboda Annabi Muhammad (SAW) ya umarce mu da mu kawar da laifi da hannun mu, idan ba zamu iya ba mu yi da harshen mu, idan ba zamu iya ba mu kyamaci abun a zuciya, amma wannan shine mafi raunin Imani."

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya magaantu kan sabon rikicin da ya ɓarke a PDP, ya faɗi matakan da suke ɗauka

Meyasa aka shirya wa Malamai horar wa?

Da yake jawabi a wurin taro, Amir na ƙasa na gidauniyar Alhabibiyya, Ustaz Adeyemi Fu’ad, ya yi bayanin cewa sun shirya taron ne don wayarwa malamai kai kan bukatar dogaro da kai da magana kan rashawa.

A wani labarin kuma Jami'an tsaro sun mamaye majalisar dokokin jiha a arewa bayan an yi yunkurin ƙonata

Jami'an tsaro sun kewaye zauren majalisar dokoki n jihar Bauchi bayan wani yunkuri na ƙona wurin bai ci nasara ba.

Wannan na zuwa ne bayan rikici ya ɓarke a majalisar, inda mambobi 22 suka bukaci kakaki ya yi murabus ko su tsige shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262