Eid-El-Kabir: Ba mu sanya jarabawa ba ranar idi, Hukumar NECO ta magantu
- Hukumar shirya jarabawar NECO ta musanta raɗe-raɗin da aka fara yaɗawa cewa ta sanya jarabawa ranar Idin babbar Sallah
- A wata sanarwa da shugaban sashin yaɗa labarai ya fitar, ya ce hukumar ta na da tsari me kyau kuma ta san muhimmancin shagulgulan Addinai
- Ya ce a jadawalin jarabawar bana 2022, ta ba da hutun mako ɗaya don ba musulmai isasshen lokaci
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Hukumar shirya jarabawa ta ƙasa (NECO) ta ce bata sanya jarabawa ranar Asabar 9 ga watan Yuli, 2022, ba, ranar da zata kama ranar babbar Sallah (Ed-El-Adha) yayin da ɗalibai ke cigaba da zana jarabawar kammala Sakandire (SSCE).
Jaridar The Nation ta ruwaito hukumar na cewa ta yi haka ne domin ba mabiya Addinin Musulunci damar samun cikakken lokaci na murnar babbar Sallah.
'Ku bi umarnin Annabi SAW' An roki Malaman Addinin Musulunci a Najeriya kar su ruɗu da kuɗin yan siyasa
Shugaban sashin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na NECO, Azeez Sani, shi ne ya yi karin haske a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 4 ga watan Yuli.
Wani sashin sanarwan ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Hukumar NECO na farin cikin bayyana cewa ba ta tsara gudanar da kowace jarabawa ba a ranar Asabar 9 ga watan Yuli, 2022."
"Wannan ya saɓa wa maganganun da wasu suka fara yi a wasu sassan ƙasa cewa hukumar ta sanya jarabawa a ranar 9 ga watan Yuni, wacce ta kama ranar idin babbar Sallah."
"Sanin muhimmancin ranaku irin waɗan nan a Addinai ya sa hukumar NECO ke da tsari mai kayu wajen sanya ranakun zana jarabawa."
Akwai hutun Sallah a jadawalin jarabawar bana - NECO
Sanarwan ta kara da cewa ta ba da hutun mako guda, daga 8 ga watan Yuli, 2022 zuwa 13 ga watan Yuli, domin ba Musulmai cikakken lokacin da zasu yi shagalin sallah, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Mayaƙan ISWAP da suka yi yunkurin kai kazamin hari Monguno da motocin yaƙi sun kwashi kashin su a hannun Sojoji
Idan baku manta ba, Ɗaliban ajin karshe a Sakandire sun fara zana jarabawar kammala makaranta, wacce NECO ke shirya wa a ranar 25 ga watan Yuni, kuma zasu ƙare a ranar 12 ga watan Agusta 2022.
A wani labarin kuma 'Daruruwan ɗalibai mata sun tsallake rijiya da baya yayin da wuta ta kama rigi-rigi a Hostel ɗin kwalejin Ilimi
Ɗalibai mata sun sha da ƙyar yayin da wata Gobara ta tashi a gidan kwanan su na kwalejin Ilimi ta Peaceland, jihar Enugu.
Rahoto ya nuna cewa wutar ta fara ne daga ɗaki guda, kuma ta aikata babbar ɓarna da ya haɗa takardun karatun Diplomar ɗalibai.
Asali: Legit.ng