Bidiyo: An tirsasa barawo yin sallah babu tsayawa bayan kama shi yana sata a masallaci

Bidiyo: An tirsasa barawo yin sallah babu tsayawa bayan kama shi yana sata a masallaci

  • Wani barawo ya shiga hannun jama'a yayin da ya je masallacin Juma'a yin sata amma sai kuma dubunsa ta ciki a ranar
  • Babu bata lokaci masallata suka kama shi tare da ladabtar da shi da yin sallah babu kakkautawa kafin a mika shi hannun 'yan sanda
  • A lokacin da aka nadi bidiyon abinda ke faruwa, an gano cewa yana kan raka'arsa ta goma ne kuma jama'a sun zagaye shi suna kallon shi

An yi ram da wani mutum da ake zargi da sata a masallaci yayin da ake yin sallar Juma'a.

Babu kakkautawa jama'a suka damke shi tare da bashi ladabtarwar da ta dace.

A matsayin ladabtarwa, an tirsasa barawon yin sallah babu tsayawa yayin da Musulmai suka zagaye shi suna kallon shi.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Amarya Ta Zage Ta Kwashi Garar Girki Kafin Ta Shiga Filin Rawa

Barawo
Bidiyo: An tirsasa barawo yin sallah babu tsayawa bayan kama shi yana sata a masallaci. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A matsayin ladabtarwa, an tirsasa barawon yin sallah babu tsayawa yayin da Musulmai suka zagaye shi suna kallon shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin da ake nadar wannan bidiyon, an rahoto cewa yana kan raka'arsa ta 10 ne.

Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai suna @HoeGee_Tyla shine ya wallafa bidiyon yayin da yake bayanin cewa za a mika wanda ake zargin da sata hannun 'yan sanda idan ya kammala sallar.

Kalla bidiyon a kasa:

'Yan Najeriya sun yi martani a kai

Babu dadewa da wallafa bidiyon, jama'a sun garzaya sashin tsokaci inda suka dinga tofa albarkacin bakunansu.

Ga wasu daga cikin tsokacin:

@fishbone cewa yayi: "Lallai wannan barawon yana da sa'a, ai wannan hukuncin yafi sassauci a kan cire masa kai ko kuma jefe shi."
@Khalil144 cewa yayi: "Sakarai mara tsoron Allah, ka rasa inda zaka je sata sai masallaci. Da ina wurin sai yayi raka'a dari sannan mu mika shi hannun 'yan sanda."

Kara karanta wannan

Bidiyon Ango Ya Zurfafa Cikin Tunani Yayin Da Amaryarsa Ke Girgijewa A Wajen Liyafar Aurensu

Taron gangamin APC: An yi ram da masu sane 3 a cikin jama’a

A wani labari na daban, jami'an tsaro sun damko mutane uku da ake zargin ƴan sane ne a dandalin gagarumin zaɓen shuwagabannin jam'iyyar APC bayan an kama su suna ƙwace wayoyi a bakin kofa, Daily Trust ta ruwaito.

Jami'in tsaron, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Asabar a Abuja, yadda waɗanda ake zargin suka yi amfani da damar cunkoson dake ƙofar shiga Eagle Square wajen kwace wayoyin mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng