Na sadaukarwa da Najeriya rayuwata: Sojan da ya rasu a farmakin Shiroro
- Daya daga cikin sojojin da suka rasa rayukansu a harin da 'yan bindiga suka kai mahakar ma'adanan da ke Shiroro a Neja ya bayyana yadda ya sadaukar da rayuwarsa ga Najeriya
- Hussaini Muhammad, daya daga cikin sojojin da suka kai dauki a harin da aka kai mahakar ma'adanan, ya bukaci 'yan Najeriya da su yi wa dakarun addu'a
- Ya fadi hakan ne a wani bidiyon da ya yi wasu watanni kafin mutuwarsa, wanda a halin yanzu ya rasu ya bar mata, 'ya'ya bakwai da iyayensa da rai
Shiroro, Neja - Daya daga cikin sojojin da 'yan bindiga suka halaka yayin harin mahakar ma'adanai tsakanin Ajata da Aboki a karamar hukumar Shiroro dake jihar Neja, a ranar Alhamis, ya ce ya sadaukar da rayuwarsa don tsare rayuwar 'yan Najeriya.
A wani bidiyo da aka wallafa a yanar gizo wasu watanni da suka shude kafin kai farmakin, sojan mai suna Hussaini Muhammadu daga jihar Jigawa ya bukaci 'yan Najeriya su yi addu'a ga dakarun da ke yaki a daji don tsare rayukan mutane.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Gafaranku dai, abokai da masoya, iyaye da kowa da kowa, wannan shi ne dajin Minna inda 'yan bindiga ke bi zuwa kauyaku, mun riga mun isa wurin.
"Saboda haka muna matukar bukatar addu'oin ku, a nan mun sadaukar da rayuwarmu ga al'umma, da iyalansu da kasa, mun zo nan ne don ceto su (kasa) da rai ko a mace," a cewar Muhammad a bidiyon.
Kanin Muhammad, Bashir ya shaidawa Premium Times yadda marigayin 'dan uwansa ya dauki bidiyon bayan an mayar da shi aiki jihar Neja.
A bidiyon, ya ce "Muna fatan dawowa da ranmu shiyasa muke bukatar addu'oinku. Za mu yi iya kokarinmu wajen tsaretar da mutane da dama gami da halaka 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane da masu yi wa mata fyade.
"Sauran abokan aikina, yanzu bana Port-Harcourt, ina dajin Neja, ban san yaushe za mu dawo ba, kawai ku yi mana addua," a cewar Muhammad a bidiyon.
Muhammad na daya daga cikin sojojin da suka kai dauki bayan samun rahoton yadda 'yan bindiga suka kai hari a mahakar ma'adanan.
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana yadda suka aukawa kwantan baunan da 'yan bindiga suka musu haka yasa jami'an tsaro da dama suka fadawa tarkonsu.
Ya rasu ya bar mata da yara bakwai da iyayensa.
Asali: Legit.ng