'Yan bindiga sun sako ma'aikatan da suka sace a Zamfara, sun maida kuɗin fansa
- 'Yan bindigan sun sako ma'aikatan lafiyan da suka yi garkuwa da su a yankin Ɗansadau, ƙaramar hukumar Maru, jihar Zamfara
- Mazauna yankin sun bayyana cewa har kuɗin fansan suka dawo da shi bayan wasu makiyaya sun shiga tsakani
- Shugaban babban Asibitin Ɗansadau, Muhammad Mansur, na ɗaya daga cikin mutanen, kuma ya tabbatar da cewa sun kuɓuta
Zamfara - 'Yan bindigan da suka yi garkuwa da ma'aikatan lafiya a jihar Zamfara ranar Asabar da ta gabata a kan babbar hanyar Gusau-Ɗansadau, sun sako su baki ɗaya.
'Yan fashin dajin, waɗan da sunan su ya fi shahara da ƴan bindiga a Zamfara da sauran jihohin arewa ta yamma da suka hana zaman lafiya, sun kuma maida miliyan N5m da aka biya su da sunan kuɗin fansar nutanen.
Premium Times ta rahoto yadda yan bindigan suka mamayi ma'aikatan lafiyan suka yi awon gaba da su, ciki har da kwararren likiti, Muhammad Mansur, shugaban babban Asibitin Ɗansadau, ƙaramar hukumar Maru.
Mansur, wanda alamu suka nuna masu jaje da murnar dawowarsa sun zagaye shi, ya tabbatar da kubutar su ga manema labarai ta wayar salula ranar Jumu'a da safe.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Meyasa 'yan bindigan suƙa sako su kyauta?
Mazaunan yankin sun ce wasu makiyaya waɗan sa suka ɗaura ɗamarar dawo da zaman lafiya a ƙauyukan Ɗansadau masu ƙasar noma, sune suka shiga tsakani.
A cewar su, shigar makiyayan cikin lamarin ne ya kawo nasarar kubutar ma'aikatan lafiya da kuma dakatar da biyan miliyan N5m da maharan suka nema.
Wani Basaraken gargajiya, Mustapha Umar, ya ce makiyayan ne suka bi bayan wanda zai kai kuɗin fansa, Sama’ila Nagogo, zuwa wurin da suka umarta, nan suka haɗu da yan bindigan suka rankaya zuwa wurin shugaban su.
'Daruruwan ɗalibai mata sun tsallake rijiya da baya yayin da wuta ta kama rigi-rigi a Hostel ɗin kwalejin Ilimi
A cewarsa, da suka je makiyayan sun nemi 'yan bindigan su saki mutanen kuma su maida kuɗin fansan, kuma ba tare da gardama ba suka aiwatar da haka.
Umar ya ce:
"An maida wa wanda ya ba da kuɗin fansan, Mamman Tsafe, wanda ƴaƴansa na cikin mutanen da aka sace. Mun fahimci yan bindigan sun yi suna a yankin amma ba su da masaniyar yarjejeniyar zaman lafiyan da aka yi."
A wani labarin kuma Dalibai mata sun tsallake rijiya da baya ta ƙananan hanyoyi yayin da wuta ta kama rigi-rigi a Hostel ɗin kwalejin Ilimi
Ɗalibai mata sun sha da ƙyar yayin da wata Gobara ta tashi a gidan kwanan su na kwalejin Ilimi ta Peaceland, jihar Enugu.
Rahoto ya nuna cewa wutar ta fara ne daga ɗaki guda, kuma ta aikata babbar ɓarna da ya haɗa takardun karatun Diplomar ɗalibai.
Asali: Legit.ng