Bai Tsinana Mana Komai Ba: Matasa Da Mata Sun Huro Wuta A Karamar Hukuma, Sun Ce Dole A Tsige Ciyaman

Bai Tsinana Mana Komai Ba: Matasa Da Mata Sun Huro Wuta A Karamar Hukuma, Sun Ce Dole A Tsige Ciyaman

  • Mata da matasa a karamar hukumar Obingwa ta Jihar Abia sunyi zanga-zangan neman a tsige shugaban karamar hukumarsu
  • Masu zanga-zangan a Mgboko sunyi ikirarin cewa ciyaman dinsu Michael Ibe Nwoke bai tsinana aikin komai ba tunda aka zabe shi don haka suka bukaci kansiloli su tsige shi
  • Sun kuma yi ikirarin cewa Nwoke ya baza yan daba a gari suna razana mutane suna kwace adaidaita sahu sannan ya kuma kori ma'aikatan karamar hukuma ga shi baya ayyukan cigaba

Abia - Ana zaman dar-dar a Mgboko, hedkwatar karamar hukumar Obingwa a jihar Abia, a jiya, yayin da mata da matasa a karamar hukumar suka yi zanga-zangan neman cire shugaban karamar hukumar, Cif Michael Ibe Nwoke kan zargin rashin yi musu aiki.

Kara karanta wannan

Buhari ya saki muhimmin sako game da zaben 2023, ya bayyana abun da zai yi

Sun bukaci kansiloli su yi amfani da dukkan hanyoyin da doka ta halasta domin tsige Nwoke daga ofishinsa, rahoton Vanguard.

Taswirar Jihar Abia
Ana Zaman Dar-Dar A Karamar Hukuma Yayin Da Mata Da Matasa Suko Huro Wuta Sai An Tsige Ciyaman. Hoto: @VanguardNGA.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An gano mata da matasa kimanin 1,000 dauke da takardu da ke dauke da rubutu mai cewa: "Michael Ibe Nwoke a matsayin shugaban ALGON ya kori ma'aikatan karamar hukuma; yi murabus ka koma kasuwancinka da wasu."

Martanin Jagoran Mata da Matasa kan Nwoke

Jagoran matan masu zanga-zanga, Hon Ijeoma Ngozi ta ce shugaban karamar hukumar ya dade yana amfani da damar da aka bashi na jagoranci ba ta hanyar da ta dace ba.

Ta ce:

"Saura wata biyar ya rage masa ya kammala wa'adinsa, amma bai yi wani abin azo a gani ba. Ba mu da ofis a nan a matsayin mu na mata, an mayar da ko ina wurin ajiye adaidaita sahu da aka kwace.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: ‘Yan bindiga sun fatattaki kauyuka 30 a Zamfara, sun sanya sabon haraji

"Yan daba suna ko ina suna kwace adaidaita sahu, suna karbar N40,000 daga hannunsu. Abin da muke gani kawai shine yan daba na razana mutane babu wani cigaba. Mun gaji da sa ido ana amfani da yaran mu wurin tada hankali."

A bangarensa, jagoran matasa, Mr Christian Nwachukwu ya ce matasa sun jefa wa Nwoke kuri'ar rashin amincewa kuma suna son ya bar ofishin.

Ya ce lokacin da Ibe Nwoke ke shuganan ALGON zagin kowa ya ke yi kuma bai yi wani aiki ba sai rikici da takwarorinsa, ginin kananan hukumar duk sun lalace.

An Rage Wa Wasu Farfesoshi Uku Mukami a Jami'ar Adamawa

A wani rahoton, Jami'ar Modibbo Adama ta Jihar Adamawa, MAU, ta rage wa wasu farfesoshi uku mukami saboda samunsu da laifuka masu alaka da karatu, Daily Trust ta rahoto.

Mataimakin shugaban jami'ar, bangaren mulki, Farfesa Muhammad Ja'afaru, ne ya sanar da hakan a bikin cika shekara uku na Farfesa Abdullahi Tukur, Shugaban MAU, a ranar Asabar a Yola.

Kara karanta wannan

Ambaliya da iska mai tsanani sun laƙume rayukan mutane, gidaje sama da 2,000 sun halaka a Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164