'Yan ta'addan Ansaru sun fi shekaru 10 suna boye a jihar Kaduna
- Dan majalisa mai wakiltar mazabar Birnin Gwari, Abubakar Umar, yace Ansaru ta yi sama da shekaru 10 a yankin
- Ya sanar da yadda suke hana karatun boko inda a halin yanzu suka haramta dukkan lamurran siyasa a yankin
- A cewar Abubakar, 'yan ta'addan sun sanya kayan sojoji kuma su rike makamai masu hatsari suna mulkar yankin yadda suke so
'Dan majalisar wakilai daga jam'iyyar PDP mai wakiltar mazabar Birnin Gwari a jihar Kaduna, Shehu Abubakar ya bayyana cewa 'yan ta'addan Ansaru sun dade suna boyewa a jihar na sama sa shekaru 10.
Abubakar ya bayyana hakan ne yayin zantawa da Channels TV a wani shiri na ranar Laraba da safe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yana magana kan umarnin kwanan nan da 'yan ta'addan suka bai wa jama'ar yankunan na haramcin shiga lamurran siyasa.
Kaduna tana fama da annobar ta'addanci a cikin kwanakin nan inda labarun hare-hare suke cika kanun labarai a kullum.
A ranar Litinin da ta gabata an kawo muku labarin yadda 'yan ta'addan Ansaru suka haramta al'amuran siyasa a yankuna gabashin Birnin-Gwari.
A yayin karin bayani kan haka, Abubakar yace: "'Yan ta'addan Ansaru suna zama a gabashin Birnin Gwari kuma sun kai shekaru 10 suna aiwatar da al'amuransu.
"A wannan shekarar ne kawai suka fara bayyana miyagun manufofinsu, suna zaman lafiya da mutane. Suna basu kariya daga hare-haren 'yan bindiga.
"A baya, suna zama a dajika. Daga baya ne bayan shekaru suka fara shigowa cikin garin Damari inda suka kusan kwace garin saboda babu 'yan sanda kwata-kwata.
"Ba mu san manufarsu ba har yanzu. Mun gano cewa sun haramta karatun boko kuma yanzu cewa suke mutanen yankin kada su shiga siyasa.
"A cikin kwanakin nan da aka yi zaben karamar hukumar, ni ne shugaban kamfen na PDP. A lokacin ne kuma PDP ta tura ni gabas duba wani aiki.
"Bayan isa ta wurin, ajen sun ja mana kunne kan cewa Ansaru sun ja kunne kan cewa kada wanda yayi siyasa a yankin.
"Sai dai muka saka injinanmu a garin gaba kuma muka sanar da ajen da su kira jama'a su zo su yi zabe."
Yace 'yan ta'addan sune ke juya yankin inda ya kara da cewa suna bayyana a kayan sojoji dauke da manyan makamai.
"Na je can shekarar s ta gabata, 'yan bindiga sun harba wani abokina. Mun je ta'aziyya. A wajen garin na ga mutane da miyagun makamai sanye da kayan sojoji.
"Sai aka ce mini Ansaru ne. Na ga sama da mutum 150 a garin a ranar," Abubakar ya kara da cewa.
Yayi kira ga gwamnati a kowanne mataki da yayi duk abinda ya dace domin samun 'yancin mutane har su yi zaben 2023 mai zuwa.
Asali: Legit.ng