Muhimman Abubuwa da ya Kamata a Sani Game da Sabon CJN Olukayode
- Shugaban kasa da Muhammadu Buhari ya rantsar Alkali Olukayode Ariwoola a matsayin mukaddashin shugaban alkalan Najeriya
- Karin girman yazo ne jim kadan bayan Tanko Muhammad ya sauka daga kujerar saboda matsalar rashin lafiyarsa
- An gano yadda hazikin Alkalin ya rike mukamai daban-daban kawo daga matakin jihohi, kasa har da tsakanin kasashe saboda tsabar kwazo gami da bajintarsa
A ranar Litinin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Alkali Olukayode Ariwoola a matsayin shugaban alkalan Najeriya na wucin gadi.
Karin girman ya zo ne jim kadan bayan shugaban alkalai, Tanko Muhammad ya sauka saboda rashin lafiyarsa.
An haifa Justice Ariwoola a ranar 22 ga watan Augustan 1958. Ya fito daga Isiyin a jihar Oyo. Ya fara karatunsa a Iseyin har zuwa kammala firamare a 1967.
Ya halarci Muslim Modern School tsakanin 1968 zuwa 1969 kafin ya koma Ansar-Ud-Deen High School, Saki, a Oyo ta Arewa a jihar Oyo.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ariwoola ya karanci shari'a a jami'ar Ile Ife wacce yanzu ta koma Obafemi Awolowo dake Ile Ife kuma ya samu digirinsa a shekarar 1980, watan Yuli.
An rantsar da Ariwoola a matsayin daya daga cikin alkalan kotun kolin Najeriya a shekarar 2011.
Ya rike mukami a matsayin daya daga cikin alkalan kotun daukaka kara tsakanin shekarar 2005 zuwa 2011 daga bisani aka yi masa karin girma zuwa babbar kotun jihar Oyo. Shi ne mutum na farko da aka nada a matsayin alkalin babban kotun jihar Oyo a shekarar 1992 daga lauya mai zaman kansa zuwa lauyan gwamnati.
Yayi aiki da tawagar lauyoyin Chief Ladosu Ladapo, SAN tsakanin Oktoba, 1998 zuwa Yuli 1989 lokacin da ya kafa kamfanin koya da kwarewa a harkar alkalanci Olukayode Ariwoola & Co a birnin Oyo tsakanin watan Agusta, 1989 har zuwa watan Nuwamba, 1992 da aka nadasa a matsayin alkali mai shari'ar kotun jihar Oyo.
Alkali Ariwoola ya rike mukamin shugaban kungiyar daraktocin kamfanin motocin Phonex Ltd - daya daga cikin hannayen jarin Oodua conglomerate tsakanin 1988 zuwa 1992.
Shugaban kungiyar yaki da fashi da makami na jihar Oyo tsakanin watan Mayu 1993 zuwa Satumba, 1996 yayin da aka aje sa wajen hedkwatar Ibadan zuwa babbar kotun Saki.
Mai girma mai shari'ar ya yi aiki a Election Tribunal a Zamfara da jihar Enugu a 1999. Sannan ya yayi aiki a kotun daukaka kara ta Port-Harcourt, Enugu, Benin, Yola da Illorin a lokuta daban-daban.
Kafin karin girmansa zuwa kotun koli, ya yi aiki a kotun daukaka kara ta Kaduna, Enugu da Legas. Sannan yana daya daga cikin mambobin kungiyar makarantar kwantar da tarzoma ta kasashe (FIDRI) inda aka ranstar da shi a Dubai, UAE a shekarar 2014.
Ya halarci karatuka da dama tsakanin kasashe da na kasa da horarwa daban-daban a Faransa, Atlanta Georgia, UK da Dubai, UAE.
Ariwoola ya yi aure kuma yana zaune cikin farin ciki da yaransa da matarsa, sannan yana kaunar karatu, sauraran wakoki masu kyau, hotuna da siyayya.
Asali: Legit.ng