Hotuna: Jastis Olukayode Ya Karba Rantsuwar Kama Aiki Matsayin Mukaddashin CJN
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Justis Olukayode Ariwoola a matsayin mukaddashin shugaban alkalan Najeriya
- Yayin rantsar da shi, Justis Ariwoola ya yi alkawarin aiki da gaskiya tare da yin biyayya ga gwamnatin tarayya
- Mukaddashin shugaban alkalan wanda ya karbi mulki daga Justis Muhammad Tanko ya kuma sha alwashin kare kundin tsarin mulkin Najeriya
FCT, Abuja -Justis Olukayode Ariwoola na kotun koli ya dauki rantsuwar kama aiki a matsayin mukaddashin shugaban alkalan Najeriya a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya rantsar da Justis Ariwoola a yayin wani biki da aka gudanar a zauren majalisa na fadar shugaban kasa da ke Abuja.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ariwoola mai shekaru 62 a duniya ya karbi aiki daga wajen tsohon shugaban alkalan kasar, Justis Tanko Muhammad.
Zai ci gaba da rikon kwarya har zuwa lokacin da majalisar alkalan kasa za ta tabbatar da shi.
Yayin da yake daukar rantsuwar kama aiki, ya yi alkawarin yin aikin cikin gaskiya da kuma biyayya ya gwamnatin tarayyar Najeriya da kuma kare kundin tsarin mulkin kasar Najeriya,
Justis Muhammad ya yi murabus daga matsayin shugaban alkalan Najeriya a daren ranar Lahadi, inda ya bayyana rashin lafiya a matsayin dalilinsa na daukar wannan hukuncin.
Hakan ya yi sanadiyar rantsar da Justis Ariwoola kasancewarsa alkali mafi girma a kotun kolin a daidai lokacin da Justis Muhammad ya yi murabus.
Rahotanni sun rahoto cewa tsohon shugaban alkalan bai da lafiya sosai har zuwa lokacin da ya yi murabus.
Justice Olukayode Ariwoola zai zama sabon Alkalin Alkalai
A wani labari na daban, A yau za’a rantsar da Justice Olukayode Ariwoola a matsayin sabon Shugaban Alkalan Najeriya CJN biyo bayan murabus din CJN Tanko Mohammad daga babbar kujerar.
Mai magana da yawun Tanko Mohammed, Ahuraka Isah, ya tabbatar da murabus din maigidansa da safiyar Litinin.
Leadership ta ruwaito cewa za’a rantsar da sabon Alkalin Alkalai misalin karfe 11 na safe. Idan ta tabbata ya zama, Justice Olukayode Ariwoola zai rike mukamin har zuwa shekarar 2028.
Asali: Legit.ng