Shari'ar da ake da Abba Kyari ba zata dauki wani dogon lokaci ba, Marwa

Shari'ar da ake da Abba Kyari ba zata dauki wani dogon lokaci ba, Marwa

  • Har yanzu dai ba'a kammala shari'ar da ake da Abba Kyari da hukumar NDLEA ba
  • Shugaban hukumar NDLEA ya bayyana cewa shari'ar da ake da tsohon mataimakin kwamishinan dan sandan ba zata dau wani lokaci ba
  • Ya bayyana haka ne yayin da aka yi hira da shi da gidan talabijin din channels

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), Janar Muhammad Buba Marwa yace shari'ar da ake da tsohon mataimakin kwamishinan dan sanda, Abba Kyari ba zata dauki wani dogon lokaci a kotu ba.

Marwa wanda ya bayyana haka a wani shirin gidan talabijin na channels ranar juma'a, yace kama sauran jami'ai biyu da ake zargi da laifin ya nuna cewa za'a gaggauta hukunci kan lamarin.

Kara karanta wannan

Bai Tsinana Mana Komai Ba: Matasa Da Mata Sun Huro Wuta A Karamar Hukuma, Sun Ce Dole A Tsige Ciyaman

"An riga an kama jami'ai biyu da ake zargi da laifin kuma an tura su kurkuku, kaga wannan yana nuni da cewa shari'ar Abba Kyari ba ata dau wani lokaci ba, "Marwa.

Abba Kyari
Shari'ar da ake da Abba Kyari ba zata dauki wani dogon lokaci ba, Marwa
Asali: Getty Images

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kara da bayyana cewa hukumar NDLEA tana bada hadin kai sosai akan lamarin, inda yace hukumomin sun yarda dari bisa dari da shari'a.

Yayin amsa wata tambaya akan yadda ake zargin cewa akwai sa hannun wasu jami'an hukumar NDLEA a harkallar miyagun kwayoyi tare da Abba Kyari, Marwa ya bayyana cewa hukumar tana karfafa jami'anta kuma jajirtattu ne akan ayyukansu.

Ya kara da cewa akwai jami'ansu da yawa da suka samu lambobin yabo saboda kin amsar cin hanci kuma karamcin su yana cigaba da kawowa hukumar sakamako mai kyau.

Sojojin Najeriya sun damke kasurgumin mai sayar wa Boko Haram kayan aiki

Kara karanta wannan

Buhari ya saki muhimmin sako game da zaben 2023, ya bayyana abun da zai yi

A wani labarin, kafar labarai ta Channels ta ruwaito cewa, rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan ta'adda shida a fagagen ayyukan ta daban-daban.

Mahukuntan sojojin sun kuma ce sojojin sun kama wasu da ke hada kai da maharan, ciki har da wani fitaccen dillalin bindigu da kuma samar da kayan aikin Boko Haram.

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwa da kakakinta, Manjo Janar Bernard Onyeuko ya fitar, hedkwatar tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel