Kebbi da Wasu Jihohi 3 da FG ta Gwangwaje da $322m na Kudin Da Abcaha Ya Wawura
- An kara jihohi hudu a cikin wadanda za su amfana daga kasafta musu $322.5 miliyan na kudin da Abacha ya sace
- Jihohin sun hada da jihohin Edo, Ondo, Enugu da Kebbi kamar yadda daraktan ANEEJ ya bayyanawa manema labarai
- 'Yan kasa na daga cikin wadanda suka amince da kula da kudin da aka gano a kasar Switzerland wadan za a rabawa talakawa da marasa karfi don magance talauci a kasar
An kara jihohi hudu na Edo, Ondo, Enugu da Kebbi cikin wadanda zasu amfana daga $322.5 miliyan na kudin da marigayi shugaban kasa, Janar Abacha ya sace.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Daraktan ANEEJ, Rabaran David Ugokor, ya bayyana hakan jiya yayin ganawa da manema labarai game da kokarin da kungiyar take wajen lura da sakin kudin.
"Al'ummar 'yan kasa na daya daga cikin wadanda suka amince da alhakin sarrafa kudin da aka gano a Switzerland daga wani kaso na NASSP wanda za a raba wa talakawa da marasa karfi na Najeriya, wanda yana daya daga cikin tsarin magance talauci na National Social Investment Programme.
"Muna bukatar a shirya taron wayar da kan al'umma don sanar da wadanda suke da alhaki kafin a fara biyan kudin. Makudan kudaden da za a biya a yankuna sun kunshi masu matsalar tsaro saboda haka duk za a duba wadanda ke da asusun banki don a tura musu kudin," a cewarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An bayyana muhimman aiyuka 2 da kudin Abacha za su iya kammalawa a Najeriya
A wani labari na daban, Mallam Garba Shehu, mataimaki na musamman ga shugaban kasa a kan yada labarai, ya ce za a yi amfani da dala miliyan 311 na Abacha da aka karbo a jiya Litinin wajen tabbatar da wasu ayyukan more rayuwa.
Kamar yadda Shehu ya bayyana kuma jaridar The Cable ta wallafa, za a yi amfani da kudin ne wajen tabbatar da aikin gada ta biyu ta Niger, manyan hanyoyin Legas zuwa Ibadan da na Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.
Sannan kuma za a tabbatar da an kammala aikin wutar lantarki na Mambilla. A ranar Litinin, 4 ga watan Mayu ne gwamnatin tarayya ta karba dala miliyan 311 daga Amurka da kuma Bailiwick Jersey.
Asali: Legit.ng