An bayyana muhimman aiyuka 2 da kudin Abacha za su iya kammalawa a Najeriya

An bayyana muhimman aiyuka 2 da kudin Abacha za su iya kammalawa a Najeriya

Mallam Garba Shehu, mataimaki na musamman ga shugaban kasa a kan yada labarai, ya ce za a yi amfani da dala miliyan 311 na Abacha da aka karbo a jiya Litinin wajen tabbatar da wasu ayyukan more rayuwa.

Kamar yadda Shehu ya bayyana kuma jaridar The Cable ta wallafa, za a yi amfani da kudin ne wajen tabbatar da aikin gada ta biyu ta Niger, manyan hanyoyin Legas zuwa Ibadan da na Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano.

Sannan kuma za a tabbatar da an kammala aikin wutar lantarki na Mambilla.

A ranar Litinin, 4 ga watan Mayu ne gwamnatin tarayya ta karba dala miliyan 311 daga Amurka da kuma Bailiwick Jersey.

An bayyana muhimman aiyuka 2 da kudin Abacha za su iya kammalawa a Najeriya
An bayyana muhimman aiyuka 2 da kudin Abacha za su iya kammalawa a Najeriya
Asali: UGC

A wata takarda da ta fito a ranar Talata, Shehu ya ce yaki da cutar corona za ta zama lamari mai matukar wuya da gwamnati bata samu kudin ba.

“Karbar wadannan miliyoyin dalolin daga kasar Amurka da Switzerland wata dama ce ta habaka kasar nan. Sun samu ne kuwa bayan an yi wa kasar ‘fashi’.

“Sauran kudaden da aka samu a shekarar da ta gabata daga Switzerland ana amfani da su wajen ciyar da ‘yan makaranta, matalauta da kuma adana hatsin kasa wanda zai yi amfani a yayin rashi.

“Ba tare da wadannan kudaden ba, yaki da COVID-19 zai yi matukar wuya.”

Hadimin shugaban kasar ya kwatanta wadannan kudin da aka dawo da su da alamar dankon zumunci a tsakanin Najeriya da Amurka.

“A shekarun da suka gabata, ana kallon gwamnatin Najeriya da gurbatacciya wacce za ta iya kara sace kudin bayan an dawo da ita. Hakan ne yasa basu dawo da kudin ba,” yace.

Ya kara da cewa, “A yau, Amurka da Ingila da sauran kasashe sun samu masu mulki a Najeriya da za su iya yarda dasu.”

KU KARANTA KUMA: An killace iyalan marigayi sarkin Kaura Namoda, an yi wa fadar feshi

A yayin jaddada kokarin gwamnatin na yaki da rashawa, ya ce lokutan da ‘yan siyasa za su dinga amfani da gwamnati a matsayin hanyar samu ya yi kaura.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel