Zunuban Ike Ekweremadu: Manyan rigingimu 4 da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ya fada ciki

Zunuban Ike Ekweremadu: Manyan rigingimu 4 da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ya fada ciki

  • Sunan tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya sake hawa kanen labarai
  • An dai kama sanatan ne tare da matarsa a kasar Birtaniya kan zargin kawo wani yaro birnin Landan don kwashe sassan jikinsa
  • Kafin wannan rigimar, dan majalisar dokokin kasar ya sha caccaka a soshiyal midiya sakamakon furucin da ya yi akan takarar Peter Obi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ike Ekweremadu ya sake fadawa a cikin wani gaggarumin matsala.

Ekweremadu wanda ya shafe tsawon shekaru 19 a zauren majalisar dokokin tarayyar Najeriya ya sha fadawa a cikin rigingimu da dama.

Ike Ekweremadu
Zunuban Ike Ekweremadu: Manyan rigingimu 4 da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ya fada ciki Hoto: Ike Ekweremadu
Asali: Twitter

A wannan zauren, Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin rigingimu da dan siyasar ya taba tsintar kansa a ciki tsawon shekaru.

1. Shan dukan tsiya a Jamus

Watakila wannan shine rikici mafi muni da Ike Ekweremadu ta taba risker kansa a ciki tsawon lokaci da ya shafe a matsayin yan siyasa.

Kara karanta wannan

Har yanzu ban samu wata sanarwa a hukumance daga ubangidana ba - Hadimin Ekweremadu

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ranar 17 ga watan Agustan 2019, an tattaro cewa Ike Ekweremadu ya ziyarci Nuremberg, kasar Jamus don halartan wani taro da yan Igbo mazauna Jamus suka shirya lokacin da wasu fusatattun matasa suka far masa.

Legit.ng ta tuna cewa wasu fusatattun yan kungiyar awaren IPOB ne suka farmaki Ekweremadu.

Ba a dade ba sai bidiyo ya bayyana a shafukan soshiyal midiya inda aka gano Ekweremadu yana kokarin neman tudun tsira a yayin harin.

2. Ya sha caccaka a soshiyal midiya kan cewa da ya yi Peter Obi ba zai kai labari ba

Wannan shine rigima na baya-bayan nan da Ekweremadu ya shiga. Jigon na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya sha caccaka a shafukan soshiyal midiya kan furucin da ya yi kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi.

Kara karanta wannan

Layukan Wayan Ekweremadu Da Na Kakakinsa A Kashe, Yayin Da Aka Kama Shi Da Matarsa A Landan

A wani bidiyo da ya bayyana a shafukan soshiyal midiya, an jiyo Ekweremadu na cewa kudu maso gabas ba za su yarda su watsar da kuri’unsu wajen zabar Peter Obi ba a babban zaben shugaban kasa mai zuwa.

An tattaro cewa ya yi furucin ne jim kadan bayan an sanar da Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar.

Sai dai kuma, furucin nasa ya ja masa mummunan suka da caccaka a shafukan soshiyal midiya.

3. Zargin rashawa, da tsare shi da EFCC suka yi

Hakazalika, a watan Yulin 2018, hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gayyaci Ekweremadu don amsa tambayoyi kan zargin rashawa.

A cewar jaridar Premium Times, gayyatar da aka yiwa Ekweremadu ya bazu awanni bayan jami’an EFCC sun kai samame gidan dan majalisar da ke unguwar Apo, Abuja.

An zarge shi da mallakar wasu kadarori a wasar waje, inda aka yi zargin ya siya wasu ta hanyar amfani da sunan wasu kamfanoni sannan wasu hadimansa na siyasa suka shige masa gaba.

Kara karanta wannan

Za a shirya wasan kwaikwayo a kan tarihin tsige Sanusi I da Sanusi II a 1963 da 2020

4. An damke Sanata Ekweremadu da matarsa kan yunkurin satar sashen jikin wani yaro

Na baya-bayan nan shine cewa hukumomi a kasar Birtaniya ta damke Ekweremadu, da matarsa Beatrice kan laifin kai wani yaro kasar don cire wani sashen jikinsa.

Hukumar yan sandan kasar ta tabbatar da labarin cewa an garkamesu a kurkuku kuma za'a gurfanar da su a kotu ranar Alhamis bayan gudanar da bincike, rahoton Skynews.

Yan sandan sun kara da cewa an kaddamar da bincike ne bayan sanar da su wasu sun kawo dan wani kasar kuma hakan ya sabawa dokar bautar zamani na Birtaniya.

Jawabin yace:

"Beatrice Nwanneka Ekweremadu, 55 (10.9.66) na Najeriya ana tuhumarta da sufurin wani mutum da niyyar cire wani sashen jikinsa."
"Ike Ekweremadu, 55 (10.9.66) na Najeriya ana tuhumarsa da sufurin wani mutum da niyyar cire wani sashen jikinsa."
"An garkamesu kuma zasu gurfana gaban kotun Uxbridge yau."

Kara karanta wannan

Mun fasa kara farashin litan man fetur, yan kasuwar mai IPMAN

"An kwace yaron hannunsu kuma ana kula da shi."

Har yanzu ban samu wata sanarwa a hukumance daga ubangidana ba - Hadimin Ekweremadu

A gefe guda, mun ji cewa wani hadimin tsohon mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya yi magana game da kama ubangidan nasa, inda yace har yanzu bai tabbatar da lamarin daga bangarensa ba.

Da yake zantawa da jaridar Vanguard ta wayar tarho a Enugu, hadimin nasa wanda ya nemi a boye sunansa ya nuna mamaki kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng