Har yanzu ban samu wata sanarwa a hukumance daga ubangidana ba - Hadimin Ekweremadu
- A yau ne aka wayi gari da labarin kama tsohon mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice a Landan
- Mahukunta a kasar Birtaniya sun sanar da kama Ekweremadu da matarsa kan zargin kai wani yaro kasar don kwashe sassan jikinsa
- Wani hadimin dan siyasar ya nuna kaduwa matuka da jin labarin, inda yace har yanzu bai samu ji daga bangaren ubangidan nasa ba
Wani hadimin tsohon mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya yi magana game da kama ubangidan nasa, inda yace har yanzu bai tabbatar da lamarin daga bangarensa ba.
Da yake zantawa da jaridar Vanguard ta wayar tarho a Enugu, hadimin nasa wanda ya nemi a boye sunansa ya nuna mamaki kan lamarin.
Ya ce:
“Ban tabbatar da komai ba. Har yanzu ina kokarin kiran ubangidan nawa ne. Har sai na ji daga gare shi, gaskiya ban san me ke faruwa ba. Yadda kowa ya gani a jaridar yanar gizo nima haka na gani. Ba ni da hurumin yin martani a kai a tsanake har sai na ji daga gare shi.”
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An damke Sanata Ekweremadu da matarsa kan yunkurin satar sashen jikin wani yaro
Mun dai ji cewa hukumomi a kasar Birtaniya ta damke tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, da matarsa Beatrice kan laifin kai wani yaro kasar don cire wani sashen jikinsa.
Hukumar yan sandan kasar ta tabbatar da labarin cewa an garkamesu a kurkuku kuma za'a gurfanar da su a kotu ranar Alhamis bayan gudanar da bincike, rahoton Skynews.
Yan sandan sun kara da cewa an kaddamar da bincike ne bayan sanar da su wasu sun kawo dan wani kasar kuma hakan ya sabawa dokar bautar zamani na Birtaniya.
Asali: Legit.ng