Mun fasa kara farashin litan man fetur, yan kasuwar mai IPMAN

Mun fasa kara farashin litan man fetur, yan kasuwar mai IPMAN

  • Yan kasuwar mai sun fasa kara farashin litan mai zuwa N180 kuma sunce za'a samu yalwar mai kwanan nan
  • Sama da watanni biyu yanzu mazauna birnin tarayya Abuja, Legas da wasu jihohi na fama da matsanancin tsadar man fetur
  • Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin karawa direbobin tankonin mai kudin safarar fetur

Legas - Kungiyar yan kasuwar mai masu zaman kansu watau IPMAN ta fasa kara farashin litan man fetur zuwa N180 daga N165 da gwamnati tayi umurnin a rika sayarwa.

Shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Chinedu Okoronkwo, ya bayyana hakan a hira da manema labarai a birnin tarayya Abuja, rahoton TheNation.

Ya bayyana cewa kungiyar ta canza ra'ayinta kuma zata bi umurnin gwamnati.

Ya bayyana cewa kamfanin NNPC ya yi alkawarin amsa bukatunsu kuma zai saki man fetur dake ajiye na tsawon kwanaki 32.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamnatin Neja ta ba da hutun kwanaki 2 don rajista da karbar PVC

Okoronkwo ya yi kira ga yan Najeriya su kwantar da hankulansu, yanzu za'a samu yalwar mai.

Scarcity
Mun fasa kara farashin litan man fetur, yan kasuwar mai IPMAN

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gaskiya ba zai yiwu mu sayar da fetur N168 ga Lita ba, IPMAN

Wahala da tsadar mai na kara tsanani a biranen Abuja, Legas da wasu jihohin Najeriya a ranar Litnin kuma gidajen mai sun cika da motoci.

Wannan na faruwa ne biyo bayan yajin aikin da mambobin kungiyar yan kasuwan mai masu zaman kansu (IPMAN) suka shiga makonnin da suka gabata.

A ranar Litnin shugaban IPMAN ya jaddada cewa ba zai yiwu su cigaba da sayar da litan mai N165 ba saboda yanzu haka N175 zuwa N178 suke sayan litan mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng