Tsadar Mai: Gaskiya ba zai yiwu mu sayar da fetur N168 ga Lita ba, IPMAN

Tsadar Mai: Gaskiya ba zai yiwu mu sayar da fetur N168 ga Lita ba, IPMAN

  • Shugaban kungiyar yan kasuwar mai ya bayyana cewa ba zai yiwu su cigaba da sayar da mai yadda gwamnati ke so ba
  • Sama da makonni uku yanzu ana fama da tsada da wahalar mai a fadin tarayya musamman Abuja da Legas
  • Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin karawa direbobin tankonin mai kudin safarar fetur

Legas - Wahala da tsadar mai na kara tsanani a biranen Abuja, Legas da wasu jihohin Najeriya a ranar Litnin kuma gidajen mai sun cika da motoci.

Wannan na faruwa ne biyo bayan yajin aikin da mambobin kungiyar yan kasuwan mai masu zaman kansu (IPMAN) suka shiga makonnin da suk gabata.

A hira da tashar Channels TV, Shugaban IPMAN na jihar Legas, Akin Akinrinade, ya yi fashin baki game da tsadar man da ake.

Kara karanta wannan

Buhari ya saki muhimmin sako game da zaben 2023, ya bayyana abun da zai yi

Yace:

Mambobin kungiyar yan kasuwar mai masu zaman kansu a Najeriya IPMAN sun rufe gidajen man su, amma ba wai yajin aiki muke ba,:
"Matsalar itace ba zai yiwu mu cigaba da kasuwanci haka ba. Kafin ka dauki mai, sai ka biya N162 ga Lita."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsadar mai
Tsadar Mai: Gaskiya ba zai yiwu mu sayar da fetur N168 ga Lita ba, IPMAN
Asali: Original

Akinrinade ya jaddada cewa ba zai yiwu su cigaba da sayar da litan mai N165 ba saboda yanzu haka N175 zuwa N178 suke sayan litan mai.

"Sannan mu kara kudin sufurin mai, N6 zuwa N8, dangane da inda za'a kai man a Legas. Idan wata jiha ce, kudin zai fi haka yawa."
"Saboda haka idan ka kara N8 kan N162, za'a samu N170 amma ita kuma gwamnati na son tilasta mu sayar da mai N165."
"Gashi man Diesel (Gas) ya yi tsada, ga kuma rashin wutar lantarki. Babu gidan mai a Legas dake amfani da kasa da litan Diesel 50 a rana."

Kara karanta wannan

Tallafin fetur: Majalisa za ta binciki Gwamnatin Buhari, ta ce an sace Naira Tiriliyan 2.9

"Saboda haka mambobinmu ba zasu cigaba da sayar da litan mai N165 ba, babu dan kasuwa mai hankalin da zai sayar da mai kasa da N180."

Asali: Legit.ng

Online view pixel