Karya ne, bamu kara wa'adin rijistan katin zabe ba, nan da mako daya zamu rufe: INEC
- Hukumar zabe ta INEC ta ce sam bata kara wa'adin yin rijistar katin zabe ba da kwanaki sittin
- A jadawalin INEC, ranar 30 ga watan Yuni, 2022 zata dakatar da cigaba da rijistar katin zaɓe a dukkan sassan Najeriya
- Kotun tarayya ta dakatar da shirin INEC na rufe yi wa yan Najeriya rijistar Katin zaɓe (CVR) yayin da babban zaɓe ke kara kusantowa
Abuja - Hukumar gudanar da zabe ta kasa INEC ta karyata rahotannin cewa ta dage ranar karshe na rijistan katin zabe da kwanaki sittin zuwa karshen watan Agusta.
Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin zabe, Aishatu Jibril Dukku, da farko ta yi maganar cewa INEC ta amince zata kara wa'adin rijistan katin zaben da kwanaki 60.
Amma Sakataren yada labaran shugaban INEC, Ritimi Oyekanmi, ya karyata maganar inda yace koma kadan hukumar bata sanar da hakan ba, rahoton Guardian.
Hukumar INEC ta jaddada cewa har yanzu ranar 30 ga Yuni ne ranar karshe na kowa mai bukatar rijista yayi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta dakatar da INEC daga rufe rijistar katin zaɓe a Najeriya
Babbar Kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC daga rufe rijistar Katin Zaɓe a ranar 30 ga watan Yuni, 2022.
The Cable ta ruwaito cewa hukumar INEC ta zaɓi ranar 30 ga watan Yuni a matsayin ranar da zata rufe damar yin Katin zaɓe (CVR) yayin da take shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2023.
Alƙalin Kotun, Mai Shari'a Mobolaji Olajuwon, ya amince da hukuncin biyo bayan sauraron buƙatun ƙungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP).
Kungiyar SERAP tare da wasu yan kishin Najeriya 86 ne suka kai ƙarar hukumar zabe INEC gaban Kotu a farkon wannan watan.
Asali: Legit.ng