An kashe akalla mutum 16 a sabon harin da aka kai jihar Benue
- Wasu tsagerun yan bindiga dadi sun sake kai hari jihar Benue kuma an yi rashin rayuka 16
- Shugaban karamar hukumar da aka kai harin yayi zargin cewa makiyaya ne suka kai musu hari
- Har ila yau, jihar Benue da wasu jihohin Najeriya na fama da matsalar yan bindiga masu garkuwa da mutane
Benue -Akalla dilolin katako timba guda goma sha shida suka rasa rayukansu a sabon harin da yan bindiga suka kai Mbagwen a karamar hukumar Guma ta jihar Benue.
Shugaban karamar hukumar Guma, Caleb Aba, wanda ya tabbatar da kisan yace kimanin karfe 7 na yammacin Litinin yan bindiga suka kai hari garin Mbagwen kuma suka fara harbin kan mai uwa da wabi, rahoton Leadership.
Yace:
"An kashe dilolin timba 16, mun tsinci gawawwaki biyar cikin mutum 16."
Bai Tsinana Mana Komai Ba: Matasa Da Mata Sun Huro Wuta A Karamar Hukuma, Sun Ce Dole A Tsige Ciyaman
"Mafi akasarin wadanda aka kashe dilolin Timba ne a ranar Litnin yayinda suka je yankar itace a dajin Mbagwen kuma yayinda suke kokarin fita aka bude musu wuta."
Ya ce sun kai kara wajen yan sanda don gudanar da bincike kan lamarin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Sun Kashe Mutum 3, Sun Tafi Da Matar Aure
Jiya mun kawo muku cewa mutane uku ne wasu da ake zargin yan bindiga ne suka bindige har lahira a karamar hukumar Batagarawa ta Jihar Katsina.
Vanguard ta kuma rahoto cewa an bindige wani mutumin a kafa yayin da yan bindigan sun sace wata mata mai suna Hawau Yusuf mai zaune a Unguwan Makera.
Wani mazaunin garin, Marwan Zayyana, wanda ya tabbatarwa Vanguard lamarin, ya ce maharan sun kai hari garin ne misalin karfe 4 na yammacin ranar Litinin, a kan babura, suka rika cin karansu ba babbaka har 4.30 a garin.
Marwan ya bada sunan wadanda aka kashe din kamar har; Aminu Abdulwahab, Musa Abubakar da Sadiq Lawal.
Asali: Legit.ng