Haramta acaba: Gwamnatin jihar Legas za ta rukurkushe babura 250 da ta kama

Haramta acaba: Gwamnatin jihar Legas za ta rukurkushe babura 250 da ta kama

  • Gwamnatin jihar Legas ta kama wasu babura da sauka saba dokar hanya da gwamnatin jihar ta gidanya
  • Gwamnatin ta fitar da sanarwa, cewa za ta murkeshe wasu babura 250 daga cikin wadanda aka kama a karshen mako
  • Gwamnatin jihar Legas ta haramta daukar fasinja a babura, tare da saka dokoki masu tsauri a kewayen jihar

Jihar Legas - Gwamnatin jihar Legas ta ce ta kammala shirin rukurkushe babura 250 da aka kama saboda saba dokar hanya ta jihar, Premium Times ta ruwaito.

A watan da ya gabata ne jihar ta haramta ayyukan baburan kasuwanci a kananan hukumomi shida a jihar, Ripples Nigeria.

Gbadeyan Abdulraheem, Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Kwamitin Kula da Muhalli na Jihar Legas ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun sake kai mummunan hari Kaduna, sun sace mutane 36

Za a murkushe babura a Legas
Saba dokar hanya: Gwamnatin Legas za ta rukurkushe babura 250 da ta kama | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa, wasu daga cikin baburan da aka kama na kamfanin jigila ne da suka saba doka yayin da suka gudanar da ayyukansu a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta bayyana cewa, wasu masu baburan ba su san da cewa an kame su ba, inda ta ce:

“Abin takaici, wasu daga cikin masu wadannan ababen hawa ba su san cewa an kwace musu babura ba, domin mahayan kan yi watsi da baburan da zarar jami’anmu sun kama su.
“A kekunan da Hukumar ta kama, 250 za a murkushe su ne a karshen mako a wurin murkushewa ta Taskforce da ke Alausa.”

Ya kuma bukaci duk masu aikin jigilar aiki da su horar da mahayan su cewa su daina daukar fasinja domin gujewa hadarin da ke tattare da kwace baburan daga gwamnatin jihar.

Mista Abdulraheem ya ce hukumar ta kuma kama masu amfani da manyan babura masu karfi wajen karya dokar hanya.

Kara karanta wannan

Yadda fasinjoji 18 suka kone kurmus a wani hatsari da afku a jihar Neja

A cewarsa:

“Hawa babbar babur mai karfi ba zai sa ka guje wa dokokin zirga-zirgar ababen hawa na jiha ba, musamman ma idan aka yi la’akari da tuki a hanya mai hannu daya, wanda ke da matukar hadari ga masu amfani da hanyar da ma masu tafiya a kafa.
"Duk wani babbar babur da ya karya dokar zirga-zirgar jiha zai fuskanci hukunci daidai da na baburan kasuwanci masu karamin karfi."

Karfin hali: ‘Yan sanda sun cafke wasu mutane 6 da ake zargin ‘yan fashin banki ne

A waniu labarin, rundunar ‘yan sanda a jihar Oyo ta cafke wasu mutane shida da ake zargin 'yan wani gungun barayin banki ne.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso ne ya bayyana haka a garin Ibadan a ranar Litinin, inda ya ce daga cikin wadanda ake zargin akwai wani ma’aikacin kwantiragi mai shekaru 29 da haihuwa na bankin.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Sai mun rukurkusa duk masu cin gajiyar rashin tsaron kasar nan

Ya kara da cewa, an kama wadanda ake zargin ne a maboyar su da ke Agara, Unguwar Odo-Ona a Ibadan a ranar 13 ga watan Yuni bayan sun kammala shirin yin fashin wani banki a washegari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.