Da Duminsa: 'Yan Ta'adda Sun Kai Farmaki Coci a Kaduna, Sun Halaka Mutum 3, Sun Sace Mutane Da Yawa
1 - tsawon mintuna
- Miyagun 'yan ta'adda sun kai sabon farmaki kan masu bauta a cocin katolika ta St. Moses dake Kajuru a jihar Kaduna
- Kama yadda aka tattaro, maharan sun bayyana da yawansu inda suka dinga harbi babu kakkautawa har suka kashe mutum 3
- Ba su tsaya a nan ba, sun kara da tasa keyar wasu masu bauta yayin da wasu kuma suka matukar jigata inda aka kwashesu zuwa asibiti
Kajuru, Kaduna - 'Yan ta'adda a ranar Lahadi sun kai mummunan farmaki kan masu bauta a cocin Katolika ta St. Moses dake Robuh a Unguwan Aku dake karama hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
An halaka masu bauta yayin da aka sace wasu masu yawa. Leadeship ta gano cewa, an mika mutum daya da ya samu rauni zuwa asibitin St. Gerald dake Kaduna.
An gano cewa, maharan sun bayyana da yawansu inda suka dinga harbi babu kakkautawa kuma a hakan ne suka sace wasu masu bauta bayan sun halaka rayuka uku tare da jigata wasu masu bautan.
Karin bayani na nan tafe...
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng
Tags: