Gwamnan Anambra Ya Bada Umurnin A Fara Yi Wa Masu Sana'ar Tura Baro Rajista A Jiharsa
- Farfesa Chukwuma Solodu, gwamnan Jihar Anambra ya bada umurnin a yi wa masu tura baro da ababen hawa na haya a jihar rajista
- Sanawar da ma'aikatar sufuri ta jihar ta fitar ya ce an bada umurnin ne domin dalilan tsaro da inganta karbar haraji na cikin gida
- Gwamnatin na Anambra ta shawarci dukkan masu ababen hawan na haya su tabbatar sun bada hadin kai ga atisayen rajistan da za a fara a ranar 2 ga watan Yuni
Jihar Anambra - Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya bada umurnin a fara yi wa masu tura baro, direbobin adaidaita sahu, direbobin bas da manyan motocci rajista a jihar.
An tattaro cewa ya dauki matakin ne domin inganta tsaro da kara samar da kuma tabbatar da suna biyan harajinsu a jihar, The Punch ta rahoto.
Na gazawa mutanena: Gwamnan Ondo ya fashe da kuka wiwi yayin binne wadanda harin coci ya ritsa da su
Sanarwar da sakataren dindindin na Ma'aikatar Sufuri ta Jihar Anambra, Mrs Louisa Ezeanya ta fitar, ya nuna cewa za a fara rajistan ne ta hanyar daukan hotuna da zanen yatsu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ezeanyi ta ce za a yi aikin ne tare da hadin gwiwar ma'aikatan tattara kudaden shiga na Jihar Anambra.
Wani sashi na sanarwar ta ce:
"Ma'aikatar Sufuri da hadin gwiwar Ma'aikatar Tattara Kudaden Shiga na Jihar Anambra, tana za ta fara rajistan dukkan masu ababen hawa na haya, masu tura baro, kananan bas, manyan motocci, tipa a jihar.
"Atisayen, wanda gwamna ya bada umurni, za a fara ne daga ranar 2 ga watan Yunin 2022 a kwashe makonni hudu ana yi. Ana umurtar dukkan masu motoccin haya da babura su bada hadin kai."
Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari
A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.
A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.
An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.
Asali: Legit.ng