Hotuna da Bidiyo: Buhari ya halarci yayen daliban makarantar horar da hafsoshin 'yan sanda a Kano
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci taron yayen hafsoshin 'yan sanda daga makarantar horar da su ta Wudil a Kano
- An yaye hafsoshin 'yan sandan a ranar Alhamis, 16 ga watan Yunin 2022 karkashin jagorancin AIG Ahmad Abdulrahman
- Buhari ya mika takobin karramawa ga dalibin mafi kwazo, Babarinde Oluwatosin tare da shugaban makarantar
Wudil, Kano - Shugaban kasa Muhammadu ya halarci yayen hafsoshin 'yan sanda da aka yi na makarantar horar da 'yan sanda dake Wudil a jihar Kano a ranar 16 ga watan Yunin 2022.
Shugaban kasa ya mika takobin karamci ga dalibin da yafi kowanne kwazo, Babarinde Oluwatosin tare da shugaban makarantar AIG Ahmad Abdulrahman.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawata Cadet ASP Abdullateef tare da sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba da Ministan harkokin 'yan sanda, Muhammad Dingyadi a taron yayen 'yan sandan.
Buhari ya saurar gabatarwa daga ministan harkokin 'yan sanda, Muhammad Dingyadi da Sifeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba.
Asali: Legit.ng