Harin cocin Ondo: Atiku ya bayar da gudunmawar miliyan N10 ga wadanda abun ya ritsa da su
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayar da gudunmawar naira miliyan 10 ga wadanda harin cocin Katolika na Owo, jihar Ondo ya cika da su
- Atiku ya kuma yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai kan masu ibadah da basu ji ba basu gani ba a daidai lokacin da suke tsaka da bauta
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma yi korafi a kan halin da tsaron kasar ke ciki, inda ya ce ya zama dole a tashi tsaye don magance lamarin
Ondo - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party(PDP) Atiku Abubakar, ya bayar da gudunmawar naira miliyan 10 ga wadanda harin ta’addanci ya cika da su a cocin Katolika na Owo da ke jihar Ondo.
Yayin da ya kai ziyarar jaje ga masarautar Owo, Atiku ya yi Allah wadai da kisan masu ibadah da aka yi a ranar 5 ga watan Yuni, jaridar Vanguard ta rahoto.
Atiku ya samu wakilcin dan takarar kujerar gwamna na PDP a zaben gwamnan jihar Ondo da aka yi, Eyitayo Jegede (SAN) da mambobin kwamitin aiki na jam’iyyar.
Da yake magana a fadar Olowo na Owo, Oba Ajibade Ogunoye, Atiku, ya yi korafi kan halin da tsaron kasar ke ciki a yanzu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
“Lamarin rashin tsaro ba batun siyasa bane kuma ya zama dole mu tashi tare da mutane domin tabbatar da ganin cewa mun fita daga yanayin da muka tsinci kanmu a ciki a kasar nan.
“Na zo nan a madadin jam’iyyata, shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, dan takarar jam’iyyarmu a zaben shugaban kasa mai zuwa, Alhaji Atiku Abubakar da mambobin jam’iyyar PDP a jihar Ondo.
“Atiku Abubakar ya bayar da umurnin cewa a saki naira miliyan 10 don maganin wadanda harin ya ritsa da su ba tare da bata lokaci ba.
“Mu zo nan don yi maku jaje kan harin ta’addanci kan cocin Katolika na St Francis Catholic, unguwar Owa-Iuwa, Owo. Muna addu’a Allah yasa kada irin haka ya sake faruwa a kasarmu.
“Ba za mu iya ci gaba a haka ba. Wannan kira ne ga dukkanmu da mu dunga lura sosai, sannan ya zama dole mu shirya kare kanmu.
“Wannan ba batun siyasa bane. Ya zama dole mu tsaya tare da mutanen da za su tabbatar da ganin cewa mun fita daga wannan yanayi da muka tsinci kanmu ciki a kasar nan.”
Yayin da yake maraba da tawagar, Olowo na Owo, Oba Ajibade Gbadegesin Ogunoye, ya yabawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP bisa wannan gudummawar da ya bayar, Leadership ta rahoto.
Oba Ogunoye, ya ce:
"Lokacin da lamarin ya faru, kun aiko da sako kuma sakon ya kwantar da hankalinmu, kuma ya zama ruwan sanyi a gare mu.
“Owo kasa ce ta zaman lafiya kuma muna karrama baki. Babu wanda ya taba cinye mu da yaki kuma ba wanda zai rinjaye mu. Mun riga mun dauki matakai don tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ba.
“Eyitayo Jegede, kai shugaba ne, mai natsuwa, mai ilimi. Kai jagora ne kuma za ka ci gaba da zama jagora.”
Harin cocin Ondo: Tinubu ya bayar da tallafin miliyan N75, ya yi kira ga inganta tsaro
A wani labari makamancin wannan, Legit.ng Hausa ta kawo a baya cewa babban jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi alkawarin aiki tare da Gwamna Rotimi Akeredolu domin kawo dauki ga wadanda harin Owo ya ritsa da su.
Da yake magana a fadar sarkin Owo, Oba Ajibade Gbadegesin Ogunoye a yayin ziyarar jaje da ya kai, Tinubu ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa bayin Allah da ke tsaka da ibadarsu, jaridar Punch ta rahoto.
Ya bayyana harin a matsayin mugunta da ya zama dole a kawo karshensa, yana mai cewa “babu hurumin irin wannan kiyayya da kashe rayukan da basu ji ba basu gani ba" a kasarmu.
Asali: Legit.ng