Yau ko gobe Juma'a: Ganduje, Shettima, da mutum biyu da ake sa ran Tinubu zai zaba

Yau ko gobe Juma'a: Ganduje, Shettima, da mutum biyu da ake sa ran Tinubu zai zaba

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC zai sanar da abokin tafiyarsa yau ko gobe
  • Alamu sun nuna cewa Bola Tinubu ya yanke shawarar zaben Musulmi daga Arewacin Najeriya
  • Daga cikinsu akwai Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon gwamnan Borno

Dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai sanar da abokin tafiyarsa ranar Alhamis, 16 ga Yuni, rahoton Vanguard.

Jaridar ta kara da cewa da alamun Tinubu ya yanke shawaran zaben Musulmi.

Amma Legit Hausa ta tattaro daga tsohon Shugaban matasan jam'iyyar APC kuma hadimin shugaba Muhammadu Buhari, Isma'il Ahmad, ya bayyana cewa an zabi wanda zai zama mataimakin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Wike Ya Saki Hoto Da Magana Mai Boyayyen Ma'ana Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa

Barista Isam'il Ahmad wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook yace mutane su daina yada jita-jita, aikin gama ya gama, sanarwa kawai ya rage.

Yace:

"Game da abokin tafiyar Jagaban, an yanke shawara tuni. Saboda haka ku daina yada jita-jita da bayyana ra'ayoyi. Za'a bayyana komai ranar Juma'a Inshaa Allah."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asiwaju Tinubu
Yau ko gobe Juma'a: Ganduje, Shettima, da mutum biyu da ake sa ran zai Tinubu zai zaba Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

Wadanda ake sa rai sune:

- Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan jihar Kano

- Kashim Shettima, Tsohon Gwamnan jihar Borno

- Alhaji Kabir Ibrahim Masari, wani dan yankin Shugaba Buhari

- Dr. Ibrahim Bello Dauda, tsohon sakataren Buhari Support Group (BSG) kuma abokin Shugaba Buhari tun yana jam'iyyun ANPP da CPC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel