Yanzun Nan: Yan bindiga sun kai kazamin hari kan mutane a kauyen jihar Neja
- Wasu tsagerun yan bindiga sun kai sabon kazamin hari jihar Neja, sun kashe aƙalla mutum uku kuma sun sace wasu sama da 30
- Rahoto ya nuna cewa maharan sun kwashe tsayin lokaci suna aikata ta'adi kan mutane, sun kona gidaje a harin na kauyen Garin Gidigore
- Ƙauyen da lamarin ya faru a yankin karamar hukumar Rafi ba shi da nisa da garin Birnin Gwari na jihar Kaduna
Niger - Miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari yankin karamar hukumar Rafi da ke jihar Neja, arewa maso tsakiya a Najeriya.
Leadership ta ruwaito cewa yayin harin, yan bindigan sun kashe aƙalla mutum uku kuma suka sace mazauna 30 a ƙauyen Garin Gidigore, ƙaramar hukumar Rafi a Neja.
Bayanai sun nuna cewa ƙauyen Garin Gidigore na da nisan kilomita kalilan zuwa garin Birnin Gwari a jihar Ƙaduna, yankin da yan bindiga ke da sansanoni daban -daban a dazukan da suka haɗa iyaka.
Haka nan, rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun kwashe dogon lokaci suna aikata mummunar manufar su kan mazauna ƙauyen a harin ranar Litinin da daddare.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayan kashewa da sace wasu mutane maharan sun kona gidajen al'umma yayin da suke cin karen su babu babbaka a ƙauyen.
Yan bindiga sun sace mutum 50 a Zamfara
Wannan na zuwa ne yan kwanaki kaɗan bayan wasu yan bindiga sun yi awon gaba da wasu baƙi da suka halarci ɗaura aure a jihar Zamfara.
Yan ta'addan sun tuntuɓi iyalan waɗan sa suka yi garkuwa da su kuma sun bukaci a tattara musu maƙudan kuɗi da suka kai miliyan N145m a matsayin fansa.
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya ce gwamnatinsa zata yi duƙ me yuwuwa don tabbatar da mutanen sun kuɓuta cikin ƙoshin lafiya.
A wani labarin kuma Bayan wani kazamin artabu, Sojoji sun samu gagarumar nasara kan yan ta'adda a Borno
Jami'an tsaro sun yi nasarar halaka yan ta'addan kungiyar ISWAP da dama a yankin Gurzum da ke jihar Borno.
Hukumar sojojin Najeriya, ranar Laraba da safe, ta bayyana cewa dakarun sun lalata kasuwa da sansanin yan ta'addan yayin samamen.
Asali: Legit.ng