Yanzu: Kamfanonin Jiragen Sama a Najeriya Za Su Tsayar Da Aiki Saboda Tsadar Man Jirgin Sama

Yanzu: Kamfanonin Jiragen Sama a Najeriya Za Su Tsayar Da Aiki Saboda Tsadar Man Jirgin Sama

  • Kungiyar Kamfanonin sufurorin jiragen sama a Najeriya, AON, ta cigaba da kokawa game da tsadar man jirgin sama wato Jet A1 a kasar
  • Allen Onyema, mataimakin shugaban kungiyar kamfanonin jiragen na Najeriya ya ce akwai yiwuwar wasu kamfanoni uku su tsayar da ayyukansu
  • Onyema ya ce ba a taba samun tsadar mai irin na yanzu ba da lita ta kai N714 yana mai cewa gwamnati tana iya kokarinta wurin tallafa musu abin ya fara fin karfinsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kawo yanzu babu alamar samun sauki game da karancin man jiragen sama (Jet A1) a Najeriya, hakan yasa Kungiyar Masu Jiragen Sama, AON, ke fargabar wasu kamfanoni 3 na jirage za su tsayar da aiki.

Duk da cewa ba a ambaci sunayen kamfanonin ba, mataimakin shugaban AON, Mr Allen Onyema, ya tabbatar da cewa man jirgin ya yi tsadar da ba a taba gani ba na N714 duk lita.

Kara karanta wannan

Kiyayya Ta Makantar Da Kai: Femi Adesina Ya Caccaki Oyedepo Kan Alkanta Gwamnatin Buhari Da Rashawa

Tsadar man jiragen sama zai saka wasu kamfanoni tsayar da ayyukansu a Najeriya.
Kamfanonin Jiragen Sama a Najeriya Za Su Tsayar Da Aiki Saboda Tsadar Man Jirgin Sama. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta rahoto cewa Gwamnatin Tarayya da Majalisar Tarayya sun sha kokarin warware matsalar a yayin da farashin na Jet A1 ke cigaba da tashi.

Ya bayyana cewa saboda mataslar, Gwamnatin Tarayya ta bada umurnin a bawa kamfanonin jiragen tan 10,000 na man jirgi amma ya ce har yanzu abin bai isa hannun su ba.

Ya ce watanni 16 da suka gabata, N200 ake siyar da lita amma ya tashi zuwa N700 a yanzu a kasuwanni.

"Hakan yasa muka nufi wurin Gwamnatin Tarayya kuma ta bamu tan 10,000 a kan N580 duk lita da N607 duk lita a wajen Legas.
"Wannan ba shine kadai matsalar ba, tun bayan annobar COVID-19, kamfanonin jirage na duniya har da Najeriya ba su farfado daga COVID-19 ba sai dai wadanda kasashensu suka basu tallafi sosai. Ba laifin kowa bane. Ya faru ne kawai. Gwamnati ta yi iya kokarinta ta bamu man. Man zai isa jirage tafiye-tafiye a Najeriya da kasashen waje.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Rikici ya barke yayin da aka kashe wani jigon jam'iyyar APC

"Wasu kamfanonin jiragen a kasar waje sun rufe saboda tsadar man jirgin. Idan ba a dauki mataki ba a Najeriya, abin zai iya shafar kamfanonin marasa karfi a kasar.
"Mun fahimci cewa kwamitin da aka kafa ba za ta iya wani abu sosai ba saboda canjin kudin kasar waje da farashin mai a duniya. Yan kasuwar na sayarwa kan yadda suka siyo ne. Farashin man jirgi ya karu, har a Landan da sauran kasashen duniya. Na mu ya yi muni saboda karin kudin canji," in ji shi.

'Za ka iya amfani da Manhajar WhatsApp ko da wayarka na kashe'

A wani labarin daban, kun ji cewa manhajar aika saƙon kar ta kwana na WhatsApp mallakar kamfanin Facebook ta sanar da fara wani gwaji da zai bawa masu amfani da manhajar daman amfani da ita ko da wayarsu na kashe, The Punch ta ruwaito.

A wani rubutu da ta wallafa a shafinta a ranar Laraba, Injiniyoyi a Facebook sun ce sabon tsarin zai bawa mutane daman amfani da WhatsApp a wasu na'urorinsu ba tare da sun sada na'urar da wayarsu ta salula ba.

Kara karanta wannan

Jerin mutane 50 da Bola Tinubu ya fito da su a siyasa har Duniya ta san da zamansu yau

Tunda aka samar da shi a 2009, Facebook ta siya manhajar aika sakonnin a wayoyin zamani, WhatsApp, wanda ke da biliyoyin masu amfani da shi a faɗin duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: