Bidiyon Yadda Mai Kwalliya Ya Maida Tsohuwa Zuwa Zukekiyar, Farar, Matashiyar Budurwa

Bidiyon Yadda Mai Kwalliya Ya Maida Tsohuwa Zuwa Zukekiyar, Farar, Matashiyar Budurwa

  • A wani bidiyo da ya yadu, an ga yadda wani matashi ya yi amfani da kwalliya wajen sauya halittar wata tsohuwa wacce mutane da dama suka kasa ganewa
  • Kwalliyar da mutumin ya mata ta boye kwarmin idon tsohuwar gami da gyara mokadewar da fuskarta tayi zuwa saita karan hancinta yadda ya dace
  • Masu amfani da kafafan sada zumunta sun ce yana da matukar mahimmanci mutane su dinga zuwa wanka da wadanda za su aura don su san yadda kamanninsu yake

Mutane ba za su gaji da magantuwa a kan mai kwalliyar da ya sauya halittar wata mata gaba daya ba.

Wani bidiyo da ya yi yawo ya tada kura a kafafan sada zumuntar zamani. A bidiyon TikTok din, an ga yadda wata mata mai kwarmin ido ta zauna gami da mika fuskarta ga wani mai kwalliya don ya yi aiki a fuskarta.

Kara karanta wannan

Hari Da Taimakon Jirgin Sama: Mazauna Kajuru Sun Bayyana Tashin Hankalin da Suka shiga

Mai Kwallaiya Ya Rangadawa Tsohuwa, Ta Koma Zukekiyar Budurwa
Bidiyon Yadda Mai Kwalliya Ya Maida Tsohuwa Zuwa Zukekiyar, Farar, Matashiyar Budurwa. Hoto daga TikTok/@ranggajuans
Asali: UGC

Mutane da dama sun yi mamakin yadda matar ta koma bayan an kammala kwalliyar.

Gaba daya kwalliyar, wacce ta dauki tsawon lokaci ana yi, a yanke ta zuwa sawu sakonni.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan shafa mata hodar shimfidar kwalliya a fuskarta, mutumin ya maida hankali a kan idanunta.

Ba tare da zato ko tsammani ba, aka nemi kwarmin idon matar aka rasa. An saita hancinta yadda ya dace.

Yayin da mai kwalliyar ya kammala aikinsa, sakamakon ba abun yarda bane, saboda yadda zai yi wahala a iya hada fuskar matar da yadda aka maidata.

Daga lokacin da aka tattara rahoton nan, mutanen da suka sake wallafa bidiyon sun kai 53,000 tare da tsokaci kusan 20,000.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin tsokacin jama'a:

abdulaibarry287 ya ce: "Wannan laifi ne ga kyau."

Kara karanta wannan

Na fece, yallabai: Wasikar murabus din wani ta girgiza jama'a a kafar intanet

Jamesetta Tolbert ta ce: "Tayi kyau, amma wannan kwalliyar ta yi haske ga fatarta. Daga baka zuwa fara?"
lovelymaeghan ta ce: "Maza ku yi hankali da wandanda za ku yi soyayya dasu. Fitar ta farko kuje iyo ku yi wanka."
Noah ya ce: "Wannan shi ne dalilin da yasa nake yawan zuwa da budurwata iyo."
fadielahtheunuss3 ta ce: "Kai gaskiya mai kwalliyar nan ya kware."

Mai da tsohuwa yarinya: Bidiyon yadda 'yan kwalliya suka sauya halittar tsohuwa

A wani labari na daban, wani bidiyon da aka yada kafafen sada zumunta na wata tsohuwa tana kwalliya ya bar baya da kura, inda mutane da yawa suka ji mamakin yadda tsohuwar ta canza zuwa kyakkyawar budurwa.

A cikin bidiyon da @arewafamilyweddings ya yada a shafin Instagram, matar ta zauna kan kujera yayin da mai mata ke mata kyakkyawan kwalliyar a fuskarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng