Zamu ceto dukkan mutanen da aka sace a Zamfara Insha Allahu, Matawalle
- Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bukaci iyalan mutanen da aka sace su kwantar da hankulan su, yan uwansu zasu kubuta
- Gwamnan ya nuna damuwarsa da ƙara taɓarɓarewar tsaro a jihar, inda ya ce gwamnatinsa ba zata runtsa ba sai mutane sun zauna lafiya
- Matawalle ya ce zasu cigaba da ɗaukar matakai ciki har da yuwuwar sake datse layukan waya a faɗin jihar
Zamfara - Kwana hudu bayan yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 50 da suka je bikin Aure a hanyar Sokoto-Zamfara a Gusau, gwamna Matawalle ya tabbatar da cewa zasu kuɓuta.
Channels TV ta ruwaito cewa Matawalle ya koka kan karuwar ayyukan yan bindiga a jihar Zamfara, inda rayuka da dama suka salwanta, wasu kuma aka yi garkuwa da su.
A wata sanarwa da Sakataren labarai, Zailani Bappa, ya fitar, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakin shawo kan matsalar tsaro a jihar.
Ya kuma buƙaci iyalan mutanen da aka sace da su amincewa gwamnati yayin da take kokarin ganin bayan ayyukan yan bindiga a jihar baki ɗaya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Premium times ta rahoto Matawalle ya ce:
"Wannan lamarin kaɗai abun takaici ne a yaƙi da ƙalubalen tsaron da muke fama da shi a jihar mu. Ina kira ga iyalan mutanen da aka sace su ƙara kwarin guiwa bisa kokarin da muke na yin me yuwuwa don kubutar da yan uwan su."
"Tuni na umarci hukumomin tsaro su gaggauta binciko wurin da maharan ke tsare da mutanen kuma Idan Allah ya so zasu kubuta."
Ba zamu lamurci ayyukan bara gurbi ba - Matawalle
A cewar gwamnan, gwamnatin jihar Zamfara ba zata lamurci ayyukan rashin ɗa'a ba daga wasu bara gurbi, waɗanda ke kokarin dagula halin da ake ciki don cimma muradan su na siyasa.
Ya kuma yi gargaɗin cewa gwamnatinsa ba zata tsaya tana kallon wasu mutane mara zuciya su riƙa cutar da al'umma ba gaira babu dalili don wata manufar siyasa.
"Nauyin mu ne gwamnati kuma ba zamu rintsa ba wajen tabbatar da kare rayuwar mutane a kowane lokaci. Ba zamu lamurci duk wata kulla-kullar siyasa da zata dagula yanayin tsaron da muke ciki ba."
"Muna da masaniyar ƙaruwar ayyukan Infoma wanda ke jawo harin yan bindiga, zamu ɗauki matakan shawo kan matsalar, haɗi da yuwuwar sake datse sabis ɗin waya a karo na biyu."
A wani labarin kuma Sojoji sun ragargaji yan ta'addan ISWAP, Sun tashi kasuwa da sansanonin su a Borno
Jami'an tsaro sun yi nasarar halaka yan ta'addan kungiyar ISWAP da dama a yankin Gurzum da ke jihar Borno.
Hukumar sojojin Najeriya, ranar Laraba da safe, ta bayyana cewa dakarun sun lalata kasuwa da sansanin yan ta'addan yayin samamen.
Karin bayani: Mutum 20 cikin yan kasuwar da aka sace a hanyar Sokoto-Zamfara sun samu yanci, 30 na tsare
Asali: Legit.ng