Kotu Ta Yanke Wa 'Mama Boko Haram' Daurin Shekaru 5 Kan Damfarar N71.4m
- Kotu ta yanke wa Aisha Alkali Wakil aka 'Mama Boko Haram' da wasu mutane biyu daurin shekaru biyar a gidan gyaran hali kan laifin damfarar miliyoyin kudi
- Hakan ya biyo bayan gurfanar da su a kotun da EFCC ta yi kan tuhumar damfarar wani Saleh Ahmed Said da suka bukaci ya kawo musu buhun wake 3000 a shekarar 2018 kan kudi N71.4m
- Bayan gabatar da hujjoji kotun ta tabbatar da aikata laifin ta yanke hukuncin sannan ta umurci a biya Ahmed Said tarar 30,500,000, rashin biyan zai janyo karin shekaru 10 a gidan yari
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Borno - Babban kotu a jihar Borno ta yanke wa Aisha Wakil da aka fi sani da 'Mama Boko Haram' hukuncin daurin shekaru biyar a gidan gyaran hali kan damfara.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da hukumar EFCC ta wallafa a shafinta a daren ranar Talata.
Hukumar yaki da rashawa da yi wa tattalin arziki ta'anatti, EFCC, reshen jihar Borno, ta gurfanar da Wakil, tare da Tahiru Daura da Prince Shoyode, a Satumban 2020 kan tuhumar aikata laifuka biyu na hadin baki da karbar kudi ta hanyar karya har N71,400,000.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wadanda ake zargin sun musanta tuhume-tuhumen da ake musu.
Tuhuma ta farko ta ce:
"Ku, Aisha Alkali Wakil, Tahiru Saidu Daura da Prince Lawal Shoyode, a yayin da ku ke shugaba, managan tsare-tsare da direktan kasa na gidanauniyar Complete Care and Aid Foundation (NGO) kamar yadda ake jero, a shekarar 2018 a Maiduguri, Jihar Borno, a karkashin hurumin kotun nan da nufin damfara, kun umurci wani Saleh Ahmed Said na Shuad General Enterprises Ltd ya kawo muku buhunan wake 3000, inda kuka gamsar da Saleh Ahmed Said cewa za ku iya biyan kudin kwangilar idan ya kammala, duk da kun san karya ne kuma kun aikata laifi karkashin sashi na 1(1) (b) da (3) na kudin laifukan damfara ta kudu da laifuka masu alaka na shekarar 2006."
Yayin gudanar da shari'ar, Muktar Ahmed, jagoran masu gabatar da karar ya gabatar da shaidu hudu kuma ya gabatar da kotu takardu da dama a matsayin hujja kan wadanda ake tuhumar.
Yayin yanke hukuncin a ranar Talata, Aisha Kumaliya, alkalin da ke shariar, ta jaddada cewa masu gabatar da karar sun gamsar da kotu cewa wanda ake tuhumar sun aikata laifukan.
Bayan samunsu da laifi, alkalin ta yanke musu hukuncin daurin shekaru biyar ba tare da zabin biyan tara.
Har wa yau, ta umurci wadanda aka yanke wa hukuncin su biya N30,500,000 a matsayin tara ga wadanda abin ya faru da shi.
Ta ce idan sun gaza biyan tarar, alkalin ta ce za su kara yin shekaru 10 a gidan gyaran halin.
Saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng