Kano: Yadda 'Dan Ta'addan ISWAP ya Samu Gidan Zama, Ya Siya Filaye 5 da Taimakon Jami'in Hisbah

Kano: Yadda 'Dan Ta'addan ISWAP ya Samu Gidan Zama, Ya Siya Filaye 5 da Taimakon Jami'in Hisbah

  • Jami'an tsaro sun yi ram da wani Malam Abba da ake zargin 'dan ta'addan ISWAP ne a jihar Kano, bayan shekaru 4 da yayi a Kumbotso
  • An gano yadda Malam Abba ya nemi taimakon wani jami'in Hisbah wurin kama haya tare da siyan filaye har biyar a wurare daban-daban a Kano
  • A cewar jami'in Hisbah, Malam Abba ya sanar da shi daga Nijar yake kuma yana kasuwancin kai takalma da sutturu, baya ga haka bashi da bayanin komai a kansa

Kano - A cikin kwanakin nan ne jami'an tsaro suka yi ram da wani 'dan ta'addan ISWAP a jihar Kano. Ya hada alaka da jami'in hukumar Hisbah a jihar wanda ya taimaka masa ya siya filaye kuma ya kama gidan haya.

'Dan ta'addan mai sunaye da yawa kamar Malam Abba da Adamu Makeri, ya hadu da jami'in hukumar Hisbah a wani darasin Larabci da yake halarta a Masallacin Almuntada, Masallacin 'yan salaf dake Dorayi a jihar Kano kamar yadda bayanan jami'an tsaro suka bayyana.

Kara karanta wannan

Hari Da Taimakon Jirgin Sama: Mazauna Kajuru Sun Bayyana Tashin Hankalin da Suka shiga

Hoton 'Dan ta'addan Boko Haram/ISWAP dauke da bindiga
Kano: Yadda 'Dan Ta'addan ISWAP ya Samu Gidan Zama, Ya Siya Filaye 5 da Taimakon Jami'in Hisbah. Hoto daga HumAnglemedia.com
Asali: UGC

HumAngle ta ruwaito cewa, alakar ta bai wa 'dan ta'addan damar kama haya a yankin Samegu dake karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano na sama da shekaru hudu kafin dubunsa ta cika a farkon watan Yuni.

Wurin yana da kusanci da inda jami'an tsaro na farin kaya suka kama wata mota dankare da makamai.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayanin ya bayyana cewa, 'dan ta'addan ya roki jami'in Hisban da yayi amfani da isar sa wurin sama masa haya bayan bayyana masa da yayi yana kwana a wata ma'ajiyar kayayyaki ne. Daga bisani ya sanar da jami'in cewa zai kwaso iyalansa daga jamhuriyar Nijar kuma yana neman taimakonsa wurin samun wani gidan haya.

"A lokacin da muka hadu, yace min shi dan kasuwar ne kuma yana kai takalma da sutturu Nijar. Bani da wani karin bayani akan miyagun ayyukan shi," jami'in Hisbah ya sanar a rahotonsa.

Kara karanta wannan

Borno: Boko Haram Sun yi Garkuwa da Mata 2 a Konduga, Kwamishinan 'Yan Sanda

Taimakon jami'in ne ya bai wa 'dan ta'addan damar samun haya ba tare da ya bi tsarikan da jihar ta gindaya ba wurin karba ko bayar da hayar gidaje.

Wani 'dan kungiyar wanda yace 'dan uwansa ne daga Nijar daga bisani ya dawo zama tare da shi. Ya yi amfani da alakarsa da jami'in Hisbah wurin siyan filaye biyar a wasu wurare a jihar.

Masu unguwanni a Kano sun yi korafin cewa masu gidajen haya da ajen suna tsallake su wurin bada haya ko siyar da gidaje ga jama'a da ba a sani ba, lamarin da ke kawo hatsari.

Legit.ng ta tuntubi wata mazauniyar karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano mai suna Hajiya Zainab Abubakar kan al'amarin.

Ma'aikaciyar bankin mai 'ya'ya 4 ta bayyana tsoro da tashin hankalin da suka shiga bayan samun labarin Malam Abba da kamensa.

"A gaskiya mun fada tashin hankali, ganin cewa abinda muke ji a nesa gashi ya zo kusa da mu. Akwai bukatar mu kiyaye kan wadanda za mu bai wa haya ko siyarwa da gidaje domin gujewa fadawa hatsari.

Kara karanta wannan

Malamin addini: Ba a taba mulkin 'yan rashawa kamar na Buhari ba a tarihin Najeriya

"Gwamnati ta riga ta gindaya sharudda da dokokin bayar da haya ko siyar da gidaje. Kamata yayi duk matsuwar da mutum ya zo maka da ita, ballantana bako, ka tabbatar an bi wadannan ka'idoji. Allah ya kare mu, ya zaunar da kasar mu lafiya," ta sanar da Legit.ng cike da alhini a muryarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng