ASUU: Dalibai Sun Koka Kan Yajin Aikin Da Ya Ki Karewa, Sun Aike Sako ga FG

ASUU: Dalibai Sun Koka Kan Yajin Aikin Da Ya Ki Karewa, Sun Aike Sako ga FG

  • A yayin da yajin aikin malamai masu koyarwa na jami'o'i ya cika wata 4, daliban Najeriya sun koka da yadda karatunsu ya tsaya cak
  • Daliban jami'ar da Legit.ng ta tattauna da su sun bayyana cewa gwamnatin tarayya bata musu adalci ba ta yadda karatunsu ya tsaya
  • Daliban sun sanar da yadda suka koma zaman gida yayin da wasu suka fara sana'a domin dogaro da kansu a maimakon wannan jiran

Yajin aikin malamai masu koyarwa na jami'o'i ya ki ci balle cinyewa yayin da ya cika watanni hudu cif tun bayan fara shi a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022.

Har a halin yanzu, babu wata takamaiman magana ko wani yunkurin janye yajin aikin da kungiyar ke yi sakamakon nuna halin ko in kula da gwamnatin tarayyar Najeriya ta nuna musu.

Kara karanta wannan

Lai: FG Ta Matukar Damuwa Da Yajin Aikin ASUU, Muna Aiki Kan Shawo Kan Shi

Daliban jami'o'in Najeriya sun koka kan yajin aikin da ya ki ci balle cinyewa
ASUU: Dalibai Sun Koka Kan Yajin Aikin Da Ya Ki Karewa, Sun Aike Sako ga FG. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Legit.ng ta samu jin ta bakin wasu daliban jami'o'i kan yadda yajin aikin ya tsayar musu da karatunsa da kuma rawar da ya taka mai kyau ko akasin hakan a rayuwarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A zantawar da Legit.ng tayi da wata dalibar jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria mai suna Yahanasu Khalid, cike da takaici ta sanar da yadda take hango kammala karatunta a shekarar nan amma abun yana neman zama mafarkin da ba zai zama gaskiya ba.

"Ni dalibar aji hudu ce da ke karantar ilimin aikin noma. A gaskiya daliban Najeriya mun shiga wani hali ganin cewa muna hango kammala karatu amma abun har yanzu shiru.
"Mun bata shekara daya tun farko sakamakon annobar korona. Mun dawo makaranta har na fara Project amma sai wannan yajin aikin ya ritsa da mu.
"Ya kamata gwamnati ta dube mu, kawayenmu da ke jami'o'in kudi duk sun kammala karatu. Mu ne aka bari a baya," ta bayyana cike da takaici.

Kara karanta wannan

Kiyayya Ta Makantar Da Kai: Femi Adesina Ya Caccaki Oyedepo Kan Alkanta Gwamnatin Buhari Da Rashawa

Sai dai dalibar ta ce ba ta yi zaman banza a gida ba koda ta koma. Ta saka kaji kuma har ta cire su, tana kokarin sake saka wasu na kiwon. Ta kuma samu aiki a wata makarantar kudi inda take koyarwa domin zaman gidan ya isheta.

"Don Allah gwamnatin tarayya ta dube mu, ta waiwayo ta biya bukatun ASUU, muna son komawa makaranta kafin mu tsufa a gida. Daga dukkan alamu hankalin gwamnati yafi karkata kan zabukan nan dake karatowa, kuma mu ne dai masu kuri'ar," ta kara da cewa

Har ila yau, Legit.ng ta samu jin ta bakin Aisha Abdullahi, dalibar aji hudu a sashen ilimin zamantakewa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, inda tace yajin aikin nan ya taba rayuwarta ta hanyoyi da dama.

"A gaskiya wannan yajin aikin ta wani fanni alheri ne. Ya bani damar zama in fahimci project dina saboda rubuta shi tare da karatu babban aiki ne a lokaci daya. Na kara da mayar da hankali wurin karatuna balle wadanda na fara a farkon zangon karatu kafin a tafi yajin aikin

Kara karanta wannan

Hari Da Taimakon Jirgin Sama: Mazauna Kajuru Sun Bayyana Tashin Hankalin da Suka shiga

"Yajin aikin nan yasa na koya tsara lokaci na. A matsayina na budurwa, ina fatan bayan kammala karatu in yi aure ne, toh zaman gidan nan ya bani damar iya kula da kannaina saboda mahaifiyata ta rasu watanni 8 da suka gabata kuma ni ce babba a gidanmu," tace.

A bangare daya kuwa, Aisha ta koka kan yadda wannan yajin aikin ya tsayar da ita daga kammala karatunta wanda zai bata damar samun kwalin digirin.

"A bangaren kwali, sakandare zan ce nake da ita. Akwai damammaki da na samu amma babu kwalin a hannu, don haka babu batun samun aikin," ta kara da cewa.

Yajin aikin ASUU: Daliban jami'a sun fusata, sun ba lakcarori da gwamnati wa'adi su bude jami'o'i

A wani labari na daban, Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) reshen kudu maso gabas ta baiwa gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) wa’adin kwanaki tara su bude dukkan jami’o’in gwamnati.

Kara karanta wannan

Jerin mutane 50 da Bola Tinubu ya fito da su a siyasa har Duniya ta san da zamansu yau

Ko’odinetan shiyyar NANS ta Kudu maso Gabas, Mista Moses Onyia, ya ba da wa’adin ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Lillian Orji, ya fitar a madadinsa, a ranar Talata a Enugu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng