Borno: Boko Haram Sun yi Garkuwa da Mata 2 a Konduga, Kwamishinan 'Yan Sanda
- 'Yan ta'addan Boko Haram sun shiga kauyen Mairari da ke karamar hukumar Konduga ta jihar Borno inda suka sace mata biyu
- Kwamishinan 'yan sandan jihar, Abdu Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace 'yan ta'addan sun hada da shanu biyu
- Ya sanar da yadda suka aike tawagar jami'an tsaro amma ba su kama su ba, ya tabbatar da cewa za a bi sahu domin ceto wadanda suka sace
Borno - Kwamishinan 'yan sanda na jihar Borno, Abdu Umar, ya ce mayakan ta'addancin Boko Haram sun sace mata biyu a kauyen Mairari da ke karamar hukumar Konduga ta jihar.
Umar ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Maiduguri. Ya ce lamarin ya faru a ranar 7 ga watan Yuni.
"Wurin karfe 7:30, wani Ari Mustapha daga kauyen Mairari a Konduga ya kawo rahoton cewa wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kutsa garinsu tare da sace 'ya'yansa biyu.
"Ya ce shekarunsu 26 da 30. Ya kara da cewa 'yan ta'addan sun sace masa shanu biyu da wasu kayansa kafin su tsere," kwamishinan yace.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Premium Times ta ruwaito cewa, kwamishinan 'yan sandan yace, bayan sun samu rahoton, sun aike tawaga yankin amma shiru ba a samu 'yan ta'addan ba.
Umar ya ce rundunar za ta tsananta nemansu har sai an ceto wadanda aka sace kuma an sada su ga iyalansu.
Kwamishinan ya yi kira ga jama'a da su kai rahoton duk wasu al'amura da ba su yarda da su ba ga hukumar tsaro mafi kusa.
Asali: Legit.ng