Na fece, yallabai: Wasikar murabus din wani ta girgiza jama'a a kafar intanet

Na fece, yallabai: Wasikar murabus din wani ta girgiza jama'a a kafar intanet

  • Wani mutum ya yada wata takarda mai sauki ta murabus daga aiki, wacce ta ja hankalin mutane da yawa saboda kasancewarta bakuwa a ido
  • Mai amfani da shafin Twitter @MBSVUDU ne ya yada wasikar da ke cewa "bye bye sir," yayin da ya yi murabus daga aikinsa
  • Da yawan jama'a sun shiga sashin sharhi sun yi raha, domin ganin wannan wasikar murabus da ta bayyana komai cikin kalmomi uku kacal

Idan ka taba aiki na kwana daya a rayuwar ka kuma ka bari, to tabbas watakila ka taba rubuta takardar murabus dinka cikin salon da aka saba dashi.

Wani kuma ya zo da salo, ya mika takardar murabus dinsa mai kalmomi uku masu sauki wadanda suka bar jama'ar soshiyal midiya baki bude.

Ajiye aiki cikin sauki
Na fece, yallabai: Wasikar murabus din wani ta girgiza jama'a a kafar intanet | Hoto: Getty Images.
Asali: UGC

Rayuwar aiki dai na da wahala. Don haka, lokacin da kake da shugaba mai ba ka wahala ko yanayin aiki mara dadi, sha'awar yin murabus a kowace rana wani abu ne da ka iya zuwa kwakwalwarka.

Kara karanta wannan

Kwastoma da abokansa sun kashe Karuwa Musulma don sun ga Al-Qur'ani cikin dakinta

Mutumin mai amfani da shafin Twitter @MBSVUDU ya yada kwafin wasikar murabus din wanda kawai ta ce "Bye bye sir," kalaman da ke nufin bankwana da mai gidansa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani lokaci fadin kalma daya mai ma'ana ta fi fadin dubbai masu cike da sarkakiya.

"A saukake."

Martanin 'yan soshiyal midiya

Masu amfani da shafin Twitter sun yi martani, inda suka bayyana ra'ayoyinsu kan shawarin mutumin. Ga kadan daga ciki:

@5Million_ ya ce:

"Ya kamata in rubuta nawa a karshen mako yayin da nake ganin wannan a yanzu"

@NtsebiH ya ce:

"Me ya kai ga dogon sakin layi idan ba ka ji dadi ba na gode."

@sakhizintombi said:

“Na aika mai layi daya. Ina mai cewa, sannu ina mai yin murabus daga aiki yau ranar karshe (na saka kwanan wata). Nagode.”

Kara karanta wannan

Allah Bai Manta Dani Ba: Bidiyon Budurwa Mai Shekaru 52 da Tayi Auren Farko

Saboda budurwa: Fitaccen dan kwallon Arsenal ya tabbatar da karbar addinin Muslunci

A wani labarin, a karshe dai mataimakin kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta maza ta Ghana, Black Stars, Thomas Partey, ya tabbatar da jita-jitar da ake yadawa na cewa yanzu ya Musulunta.

A wata ‘yar gajeriyar hira da Nana Aba Anamoah, Thomas ya bayyana cewa ya yanke shawarar sauya addini ne saboda yana kaunar budurwarsa kuma babu bambanci tsakanin Kiristanci da Musulunci.

A cewarsa: "Ina da yarinyar da nake so, na san 'yan matan kodimo na za su rabu da ni amma ba matsala ... Na girma tare da Musulmai don haka a karshen dai abu daya ne."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.