Karin bayani: Jerin Sunayen Fasinjojin Jirgin Kasan Abj-Kd da 'Yan Ta'adda Suka Saki
- A kalla fasinjoji 11 ne suka kubuta daga hannun 'yan ta'addan da suka bude wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wuta a watan Maris
- Tukur Mamu ya bayyana sunan fasinjojin da aka sako inda yace Buhari, shugaban ma'aikatan tsaro, Gumi da hukumomin tsaro abun yabo ne
- Daga cikin fasinjojin da aka sako akwai Amina Ba’aba Mohammed, Rashida Yusuf Busari, Jessey John, Hannah Ajewole, Amina Jibril
Kaduna - A kalla fasinjoji goma sha daya ne da aka sace a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Maris suka samu 'yancinsu a yau Asabar.
Fasinjojin da aka yi garkuwa da su sun kwashe kwanaki sama da 70 a hannun miyagun kafin su sako su bayan tsananin sasanci da aka yi da su.
Daily Trust ta ruwaito cewa, 'yan ta'addan sun sako fasinjojin shida mata da maza biyar a ranar Asabar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mawallafin jaridar Desert Herald, Tukur Mamu, shi ya kasance mutum na tsakiya a sasancin da ya kai ga aka sako su.
Sunayen wadanda aka sako su ne:
Amina Ba’aba Mohammed
Rashida Yusuf Busari
Jessey John
Hannah Ajewole
Amina Jibril
Najib Mohammed Dahiru
Hassan Aliyu
Peace A. Boy
Danjuma Sa’idu
Gaius Gambo
Mamu, wanda bai bayyana sunan fasinja na 11 ba a yayin rubuta wannan rahoton, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugaban ma'aikatan tsaro tare da sauran hukumomin tsaro ya dace a jinjinawa kan rawar da suka taka kafin a sako fasinjojin.
Ya kara da cewa, Sheikh Ahmad Gumi ya taka rawar gani a wannan lamarin.
"Tun daga rana ta farko da na fara, da hannunsa, na amince zan yi aikin ne saboda umarninsa. Ko a yarjejeniya ta karshe kan yadda da inda za a kai wadanda aka sace din duk da shi a ciki," yace a kan Gumi.
Tun farko, wadanda suka sace fasinjojin sun bukaci a sako musu 'ya'yansu takwas da ke hannun gwamnatin tarayya kafin su fara sako fasinjojin.
Legit.ng ta tuntubi daya daga cikin iyalan fasinjojin da aka sace a Kaduna, ta sanar da cewa babu 'yar uwarta daga cikin wadanda aka saka.
Ta bukaci da a taya su da addu'a domin hankulansu sun fara kwanciya ganin cewa sasanci tsakanin gwamnatin tarayyan da 'yan ta'addan ya fara haifar da 'da mai ido.
Bayan kwanaki 74, an sako mutum 11 cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna
A wani labari na daban, 'yan ta'addan da suka kai har jirgin kasan Abuja-Kaduna sun sako wasu daga cikin mutum sama da sittin da suka kwamushe ranar 28 ga Maris, 2022.
Mai gidan jaridar Desert Herald, Tukur Mamu, wanda ya bayyana hakan yace mutum goma sha daya (11) aka sako ranar Asabar, 11 ga Yuni, 2022., rahoton Daily Trust.
Asali: Legit.ng