An Rage Wa Wasu Farfesoshi Uku Mukami a Jami'ar Adamawa
- Jami'ar Modibbo Adama ta Jihar Adamawa, MAU, ta hukunta wasu farfesoshi uku ta hanyar rage musu girma
- Farfesa Muhammad Ja'afaru, Mataimakin shugaban jami'ar, bangaren mulki, ne ya sanar da hakan wani taro da aka yi a Yola
- Farfesa Ja'afaru ya ce jami'ar ta dauki matakin ne bayan an gudanar da bincike an kuma gano sun aikata laifi da ya shafi harkar karatu
Jihar Adamawa - Jami'ar Modibbo Adama ta Jihar Adamawa, MAU, ta rage wa wasu farfesoshi uku mukami saboda samunsu da laifuka masu alaka da karatu, Daily Trust ta rahoto.
Mataimakin shugaban jami'ar, bangaren mulki, Farfesa Muhammad Ja'afaru, ne ya sanar da hakan a bikin cika shekara uku na Farfesa Abdullahi Tukur, Shugaban MAU, a ranar Asabar a Yola.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce an mika batun ga sashin hukunta masu laifi a jami'ar kuma aka amince da rage wa malaman da abin ya shafa mukami.
"Wannan na cikin nasarorin da Tukur ya samu saboda baya lamuntar rashin da'a a jami'ar tunda ya zama VC," in ji shi.
Jaafaru ya ce nan bada dadewa ba jami'ar za ta aiwatar da dokoki na hukunta laifukan lalata tsakanin malamai da dalibai, a yanzu ana jiran amincewa ne.
"Ta zarar kwamitin ta amince da shi, zai magance duk wani batun neman lalata da malamai ke yi, maza ko mata.
"Muna fata da zarar an yi dokar, malamai da dalibai za su rika samun yadda za a warware musu matsalolinsu cikin gaggawa," in ji shi.
Ja'afaru ya kara da cewa an samu nasarori sosai a karkashin jagorancin Tukur a bangarorin samar da kudin shiga, noma, walwalar dalibai da malamai, da amincewa kwasakwasai fiye da kashi 92 cikin 100 a jami'ar.
Asali: Legit.ng