2023: Matasan Igbo Na Son Ohanaeze Ta Nemi A Bawa Yankinsu Mataimakin Shugaban Kasa
- Matasan Igbo karkashin kungiyar Ohanaeze Ndigbo sun yi kira ga yan siyasa na yankin su mayar da hankali wurin samar da tsaro
- Matasan ta bakin Cif Chinedu Arthur-Ugwa sun ce sun wakilta kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta tattauna da masu ruwa da tsaki don ganin mukamin da za a bawa igbo a gwamnati mai zuwa
- Matasan sun ce sun wakiltar Ambasada George Obiozor ya jagoranci tattaunawar yayin da sauran yan siyasan yankin su dawo su mayar da hankali don samar da tsaro
Gabanin babban zaben shekarar 2023, Kungiyar Ohanaeze Ndigbo reshen matasa ta gargadi yan siyasa daga yankinsu su mayar da hankali kan kallubalen tsaro a Kudu maso Gabas fiye da neman a basu takarar mataimakin shugaban kasa, rahoton Daily Trust.
Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa a ranar Juma'a, Cif Chinedu Arthur-Ugwa, Shugaban Matasan Ndigbo na Kudu maso Kudu, ya ba a kyalle shugabanin Ohanaeze Ndigbo na duniya karkashin jagorancin Ambasada George Obiozor su yi tattauna kan duk wani mukami da ya dace a bawa Igbo a zaben 2023.
Matasan Igbo sun bukaci yan siyasa su mayar da hankali wajen samar da tsaro a yankin
Ya bukaci yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki su mayar da hankali wurin ganin an dawo da zaman lafiya a yankunan da ake zaman dar-dar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kungiyar matasan ta nuna damuwa kan karuwar rashin tsaro a kasar Igbo, ta shawarci masu ruwa da tsaki su kira taron tsaro don ganin yadda za a magance garkuwa da mutane da sauran laifuka.
Ya yi tir da yadda wasu kungiyoyin Igbo ke kawo rabuwar kawuna suna amfani da sunan Ohanaeze domin neman wani bukata na kansu a maimakon abin da zai kawo zaman lafiya da tsaron dukkan Igbo.
Ya ce:
"Abin takaici ne yadda wasu yan siyasa tuni sun fara neman kujerar mataimakin shugaban kasa a lokacin da rashin tsaro ke karuwa a kasar Igbo, me za ka iya yi idan ba tsaro? wa zai yi mulki idan ba tsaro, kowa ya yi aiki don samar da zaman lafiya a kudu maso gabas a yanzu.
"Mun wakilta Ohanaeze Ndigbo karkashin jagorancin Ambasada George Obiozor, ya wakilci mu wurin tattaunawa don ganin mukamin da ya dace da Igbo a gwamnati mai zuwa yayin da muke kokarin samar da zaman lafiya."
Asali: Legit.ng