Saura kiris a yi garkuwa da gawar Deleget din Jigawa da ya mutu a taron APC

Saura kiris a yi garkuwa da gawar Deleget din Jigawa da ya mutu a taron APC

  • Yan bindiga sun sake tare babban titin Abuja zuwa Kaduna ranar Talata don garkuwa da matafiya
  • Daga cikin wadanda ya kusa rutsawa da su akwai wadanda suke tafiyar da gawar Deleget din da ya rasu a taron APC
  • Daga baya sai da suka canza hanya suka koma ta Nasarawa zuwa Plateau zuwa Bauchi sannan zuwa Jigawa

An yi yunkurin awon gaba da gawar Isah Baba-Buji, deleget din jihar Jigawan da ya mutu wajen zaben fidda gwanin yan takaran kujeran shugaban kasa All Progressives Congress (APC) a Abuja.

Premium Times ta ruwaito cewa an yi kokari sace gawar ne yayinda take hanyarta zuwa Jigawa don jana'iza.

Marigayin ya kasance mataimakin shugaban jam'iyyar APC na yankin Arewa maso yamma.

Jami'in karamar hukumar Buji, Ali Safiyanu, ya bayyana cewa wasu yan bindiga sun taresu a hanyar Abuja-Kaduna.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

Yace hakan ya tilasta musu juyawa suka koma Abuja da wuri.

Yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Sun koma Abuja kuma nan suka kwana, washe gari suka bi ta Nasarawa-Plateau-Bauchi, sannan suka isa Jigawa daren Laraba."
"An birneshi da daren Laraba a karamar hukumar Birnin Kudu."

Janaiza
Saura kiris a yi garkuwa da gawar Deleget din Jigawa da ya mutu a taron APC Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Deliget din Jigawa ya yanki jiki, ya fadi matacce

Kun ji cewa Alhaji Isah Baba Buji ya rasu yayin da yake wurin taron zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam'iyyar a Abuja.

Ya fadi ya mutu ne sakamakon bugun zuciya a safiyar ranar Talata a ofishin hulda da jama’a na jihar Jigawa da ke Abuja.

An ce ya fadi ne a lokacin da yake shirin zuwa dandalin Eagle Square, inda za a yi zaben fidda gwani tare da wasu wakilai daga jihar.

Ya mutu ya bar mata biyu da 'yaya 16.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng