Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutum 3 Da Suka Yi Wa Yar Shugaban Afenifere Kisar Gilla

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutum 3 Da Suka Yi Wa Yar Shugaban Afenifere Kisar Gilla

  • An yanke wa mutum uku hukuncin kisa kan kashe Olafunke Olakuri, yar shugaban kungiyar yarbawa ta Afenifere
  • Alkalin kotun, Mai Shari'a William Olamide, amma, ya wanke mutum na hudu da ake zargi, Auwala Abubakar, kakakin Miyetti Allah
  • Yan bindiga sun halaka Olufunke ne a watan Yunin shekarar 2019 a garin Ore a karamar hukumar Odigbo na Jihar Ondo

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Ondo - Kotu ta yanke wa mutane uku da aka samu da hannu a kisar Olufunke Olakuri, yar shugaban kungiyar Afenifere, Pa Reuben Fasoranti, hukuncin kisa ta hanyar rataya.

The Nation ta rahoto cewa wata babban kotu da ke zamanta a Jihar Ondo ne ta yanke hukuncin.

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Mutum 3 Da Suka Yi Wa Yar Shugaban Afenifere Kisar Gilla
Kotu ta yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kashe yar shugaban Afenifere. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Zamfara: Sarkin Da Yafi Kowanne Sarki Dadewa Yana Sarauta Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Alkali da ke shari'a, Mai Sharia William Olamide, ya wanke mutum na hudu cikin wadanda ake zargin, Auwala Abubakar, wanda shine kakakin Miyetti Allah.

Yan bindiga ne suka harbe Olufunke a Yunin shekarar 2019 a Ore, karamar hukumar Odigbo a Jihar Ondo.

An birne ta makonni kadan bayan kisar gillar da aka yi mata.

Daga bisani, an kama mutanen da ake zargin su suka kashe ta, aka kuma gurfanar da shi a kotu.

Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

A wani labarin, Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.

Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Matashi ya gurfanar kan satar Baro a Bauchi, an yanke masa hukuncin wata 7

Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel