Matashi ya gurfana kan satar Baro a Bauchi, an yanke masa hukuncin wata 7

Matashi ya gurfana kan satar Baro a Bauchi, an yanke masa hukuncin wata 7

  • An damke wani matashi a jihar Bauchi kan laifin satar baron da ake amfani wajen aikin dako
  • Kotun Shari'a dake jihar ta yanke masa hukuncin daurin watanni bakwai a gidan kurkuku
  • Jihar Bauchi na daya daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da akwai kotunan Shari'ar Musulunci

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A jihar Bauchi, an gurfanar da wani matashi mai suna AbdulJalal Sadiq kan laifin satar Baron dako.

Leadership ta ruwaito cewa an gurfanar da shi ne gaban kotun Shari'ar ta II dake jihar.

Bayan amsa laifinsa, Alkalin mai shari'a, Mukhtar, ya yankewa Abduljalal Sadiq hukuncin daurin watanni bakwai a gidan kaso .

Alkalin ya bashi zabin biyan tara N7,000 da bulala 12 gaban kotu.

Matashi ya gurfanar kan satar Baro a Bauchi, an yanke masa hukuncin wata 7
Matashi ya gurfanar kan satar Baro a Bauchi, an yanke masa hukuncin wata 7
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel