Karya yan sanda suke, harin gayya aka kai mana Ondo: Sarkin Hausawa

Karya yan sanda suke, harin gayya aka kai mana Ondo: Sarkin Hausawa

  • Sarkin Hausawan Ondo ya karyata kwamishanan yan sanda jihar Ondo kan harin da aka kaiwa Hausawa
  • An kashe mutum biyar a unguwar Hausawa dake jihar Ondo biyo bayan harin da aka kai Cocin Katolika
  • Kakakin yan sanda jihar, SP Funmilayo Odunlami, tace ba hari aka kaiwa Hausawa ba, yan fashi ne

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Akure - Sarkin Hausawan Ondo, Alhaji Abdulsalam Yusuf, ya bayyana cewa harin da aka kai unguwar Hausawa a Ondo ba fashi da makami bane kamar yadda yan sanda ke ikirari.

Alhaji Abdulsalam yace harin gayya aka kaiwa Hausawa da gayya kuma an kashe mutum biyar, Daily Trust ta ruwaito.

Akalla mutum hudu suka rasa rayukansu a harin da aka kai unguwar Sabo yayinda aka kashe mutum daya a unguwar Igba.

Ya ce al'ummar Hausa/Fulani na zaman dar tun harin da wasu yan ta'adda suka kai cocin St Francis’ Catholic dake Owo.

Kara karanta wannan

Rundunar yan sanda ta karyata batun kai harin ramuwar gayya kan al’umman Hausawa a Ondo

Karya yan sanda suke, Da gayya aka kashe mana yan'uwa a Ondo: Sarkin Hausawa
Karya yan sanda suke, Da gayya aka kashe mana yan'uwa a Ondo: Sarkin Hausawa
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa:

"Muna watsi da jawabin yan sanda; karya ne cewa yan fashi ne. Babu abinda suka dauka, kawai hari suka kai unguwannin Hausawa biyu."
"Mutum hudu suka rasa rayukansu a unguwar Sabo dake Akure - mutum biyu Hausawa ne kuma biyu Yarabawa ne yayinda suke wajen mai shayi cin Indomie. Maharan basu dauki komai ba, kuma basu amshi abu hannun kowa ba."
"Hari na biyu an kai Igba. An kashe mai suya daya. Saboda haka ba barayi bane, hari aka kawo wa Hausawa a Ondo."

Da farko kakakin yan sanda jihar, SP Funmilayo Odunlami, tace ba hari aka kaiwa Hausawa ba, yan fashi ne.

Yan bindiga sun harbe mai shayi, direba da 'yan kasuwa a jihar Ondo

Wasu ‘yan bindiga da ke barna a kan babura sun harbe wasu mutane hudu da suka hada da masu sayar da shayi da wani direba da kuma ‘yan kasuwar gefen hanya har lahira.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Yan bindiga 'A jirgin Helikwafta' sun halaka dandazon mutane a Kaduna

Kisan ya faru ne a kusa da Sabo da Igba a cikin garin Ondo a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.

Wata majiya ta ce wasu ’yan kungiyar asiri ne suka kai hari kan wata kungiyar asirin.

An tattaro cewa, wani direban kasuwa da ya tsaya cin abinci a yankin an harbe shi shima har lahira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng