Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun aika mummunar ɓarna a sabon harin Kaduna, sun kashe sama da rai 30
- Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari kan mutanen da basu ji ba basu gani a ƙaramar hukumar Kajuru, jihar Kaduna
- Bayanai sun nuna cewa aƙalla mutum 32 ne suka rasa rayukan su, yayin da mazauna ƙauyuka huɗu suka bar gidajen su
- Wata majiya daga hukumomin tsaro ta ce dakarun soji sun kai ɗauki kuma sun yi nasarar dakile harin
Kaduna - Channelst Tv ta rahoto cewa aƙalla mutum 32 suka rasa rayukan su a wasu hare-haren da yan bindiga suka kai ƙauyuka hudu a ƙaramar hukumar Kajuru, jihar Kaduna.
Kauyukan da wannan ɗanyen aikin yan ta'addan ya shafa sune Unguwan Gamu, Dogon Noma, Ungwan Sarki da kuma Maikori.
Har yanzun hukumar yan sanda ba tace uffan ba game da hare-haren, amma hakimin Kufena, Titus Dauda, ya shaida wa jaridar cewa yan ta'addan sun kai samamen ne ranar Lahadi.
Ya ce akalla mutum 32 ne suka rasa rayukan su yayin da maharan suka yi kaca-kaca da wata Coci da wasu gidaje da dama a harin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Vanguard ta ruwaito Hakimin ya ƙara da bayyana cewa:
"Da farko yan bindigan sun kai samame kauyen Dodon Noma da safiyar Lahadi, inda suka kashe mutane da yawa mafi yawan su maza."
"Daga nan suka wuce kauyukan Ungwan Gamu da Maikori suka halaka mutane kuma suka kona gidaje da dama."
Mista Dauda ya ce a halin yanzun sun yi wa dukkan gawarwakin jana'iza yayin da mazaunan waɗan nan ƙauyuka suka yi takansu domin gudun sake farmakan su.
Yadda harin ya faru
Wani mazaunin ɗaya daga cikin kauyukan, ya yi iƙirarin cewa sun hangi jirgin Helikwafta na harbin mutane daga sama, yayin da yan bindiga na bin mutanen da ke kokarin guduwa suna harbi.
Sai dai wata majiya mai ƙarfi daga jami'an tsaro ta musanta ikirarin, inda ta bayyana cewa Sojoji sun tarbi yan ta'addan ta sama da ƙasa.
Majiyar ta ƙara da cewa bayan musayar wuta bisa tilas maharan suka gudu daga yunkurin kai farmakin.
A wani labarin kuma Gwamna Fintiri ya saka dokar hana fita a kananan hukumomi biyu na jihar Adamawa
Gwamnan ya ce gwamnati ba ta da wani zaɓi biyo bayan ƙara ruruwar wutar rikicin kabilanci a yankunan da wasu sassan Gombe.
Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta ce ta baza komarta ko ina a yankin don kama bara gurbin da basu kaunar zaman lafiya.
Asali: Legit.ng