Mayakan Boko Haram sun farmaki Borno, sun sace fasinjoji masu yawan gaske

Mayakan Boko Haram sun farmaki Borno, sun sace fasinjoji masu yawan gaske

  • Mayakan Boko Haram sun farmaki kauyen Lawan Mainari da ke kusa da garin Mainok hanyar Damaturu-Maiduguri a jihar Borno
  • Yan ta'addan sun kuma sace fasinjoji da dama a harin wanda ya afku a daren ranar Litinin, 6 ga watan Yuni
  • An kuma tattaro cewa yan ta'addan sun kona manyan motoci guda tara cike da kayan abinci da tankar mai

Borno - Wasu da ake zaton yan ta’addan Boko Haram ne sun kai hari kauyen Lawan Mainari da ke kusa da garin Mainok hanyar Damaturu-Maiduguri a jihar Borno a ranar Litinin, 6 ga watan Yuni.

A cewar wani ganau, lamarin ya faru ne a wani gari da bai wuce nisan kilomita 40 ba daga Maiduguri, babbar birnin jihar Borno, Channels tv ta rahoto.

An tattaro cewa yan ta’addan sun sace matafiya da dama yayin da suka kona motoci da manyan motoci tara da ke dauke da kayayyakin abinci.

Kara karanta wannan

Samun wuri: 'Yan ta'addan IPOB sun banka wa motar siminti wuta a jihar Kudunci

Mayakan Boko Haram sun farmaki Borno, sun sace fasinjoji masu yawan gaske
Mayakan Boko Haram sun farmaki Borno, sun sace fasinjoji masu yawan gaske Hoto: Channels tv
Asali: UGC

Koda dai hukumomi basu riga sun yi martani kan lamarin ba, matafiya da dama da ke bin hanyar sun tsaya a kauyukan da ke kusa da wajen yayin da wasu suka koma Damaturu, babbar birnin jihar Yobe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wani mai mota da ya tsallake rijiya da baya a harin, Mohammed Abdullahi ya ce:

“Lamarin ya afku ne da misalin karfe 9:00 na safe, inda aka gano wasu ayarin yan ta’adda suna tsallaka hanyar da zai sada mutum da dajin Sambisa.
“Koda dai, sai da nayi gaggawan juyawa zuwa Maiduguri a lokacin da na lura cewa yan ta’addan sun bude wuta kan wasu manyan motoci cike da kayayyakin abinci, ciki harda wata tankar man fetur wanda shima sun kona shi.
“Abun bakin ciki, ina zaton cewa mayakan sun sace wasu fasin joji da masu motoci.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun shiga Abuja da sanyin safiya, sun sace mutane da dama

Samun wuri: 'Yan ta'addan IPOB sun banka wa motar siminti wuta a jihar Kudunci

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta ce ta ceto tare da kashe gobarar da ta tashi a wata babbar mota makare da buhunan siminti a yankin Nsukka na jihar Enugu.

Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne, sun banka wa motar wuta a yayin da suke aiwatar da kakaba haramtacciyar dokar zaman gida a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Daniel Ndukwe, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin a Enugu cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin, 6 ga watan Yuni, a kan titin 9th-Mile-Nsukka-Obollo Afor.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng