Harin Cocin Katolika: Mun tsince Bama-bamai uku da basu tashi ba, Yan sanda

Harin Cocin Katolika: Mun tsince Bama-bamai uku da basu tashi ba, Yan sanda

  • Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa jami'anta sun tsince bama-bamai uku da basu tashi ba a Cocin Katolikan Owo
  • A cewar Sifeton yan sanda, jami'ansa sun gano harsasan AK-47 a cikin cocin da aka kashe mutane
  • Kwana biyu bayan kai harin, har yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin kuma ba'a san makasan ba

Abuja - Hukumar yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ta samu bama-bamai uku da basu tashi ba a cikin cocin Katolika dake garin Owo, jihar Ondo, Kudu maso yammacin Najeriya.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Kakakin hukumar yan sanda na kasa, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar.

A cewarsa, masu bincike sun tsince harsasai bindigar Ak-47 da aka yi amfani wajen hallaka rayukan masu bauta.

Yace:

"Bisa binciken da muka fara gudanarwa, yan bindigan sun kai hari cocin ne da makamai da bama-bamai."

Kara karanta wannan

Buhari ya yi Allah wadai da harin cocin Ondo wanda ya kai ga kisan masu ibada

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Masu bincike na hukumar yan sanda na cikin wadanda suka fara dira wajen kuma sun ga harsasai AK-47 yayinda aka gano bama-bamai guda uku da basu samu tashi ba."
"Yan bindigan sun gudu daga wajen cikin mota Nissan Sunny mai lamba AKR 895 AG wacce suka kwace hannun wani, kuma suka tsere ta titin Owo/Ute. An gano motar kuma mai ita na wajen yan sanda wajen bincike."

Akeredolu
Harin Cocin Katolika: Mun tsince Bama-bamai uku da basu tashi ba, Yan sanda Hoto: Rotimi Akeredolu
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel