Da Dumi-Dumi: Bayan shekara hudu, Kamfanin jiragen sama na Najeriya ya samu lasisin fara aiki
- Daga karshe bayan tsawon shekara hudu, Nigeria Air ya samu lasisin fara aikin jiragen sama daga hukumar NCAA
- Ma'aikatar sufurin jiragen sama ta ƙasa ta sanar da cewa ta karbi lasisin ALT kuma zata sanar da lokacin fara jigilar fasinja nan ba da jimawa ba
- Tun a watan Maris, Nigeria Air ya cike neman lasisin a hukumar NCAA biyo bayan bukatar gwamnatin tarayya na jawo masu zuba hannun jari
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Kamfanin jiragen sama mallakin gwamnatin tarayya, 'Nigeria Air' ya karɓi lasisin fara ayyuka (ALT), shekara hudu bayan baayyana shi.
Wannan na ƙunshe a wata sabuwar sanarwa da ma'aikatar kula da sufurin jiragen sama ta ƙasa ta fitar a shafinta na dandalin twitter.
An samu wannan cigaban ne bayan dogon lokaci tsawon shekara hudu da ƙaramin ministan sufurin jiragen sama, Hadi Siriki, ya kaddamar da shirin fara aikin kamfanin.
Tun a jiya Lahadi, Ma'aikatar ta bayyana cewa kamfanin jiragen zai karbi lasisin aiki ALT ranar Litinin daga hannun hukumar kula da ayyukan jirage ta ƙasa NCAA ranar Litinin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Biyo bayan karban lasisin a babbar hedkwatar NCAA da ke Abuja, ma'aikatar ta yi amfani da shafin Twitter don sanar wa yan kasa da cigaban.
Sanarwan ta ce:
"An gabatar da takardar lasisin ALT ga kamfanin Najeria Air, muna taya murna. Yanzu Nigeria Air ya gama shiryawa kuma zai yi aiki nagari ga yan ƙasa."
Yaushe jirage zasu fara aiki gadan-gadan?
Da yake tsokaci kan cigaban, Sirika ya ce nan ba da jimawa ba za'a sanar da lokacin fara jigilar jiragen.
"Kamfanin Nigeria Air ya ƙarbi lasisin ALT daga hukumar NCAA domin samun damar fara harkokin tashin jiragen sama. Zamu sanar da lokacin fara jigila a hukumance."
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa tun a watan Maris, Kamfanin ya cike neman lasisi a hukumar NCAA domin fara aikin jigilar fasinjoji.
Hakan ta faru ne bayan gwamnati ta buɗe zuba hannun jari ga masu zaman kan su da kuma ɓangaren gwamnati.
Ta kuma ƙara da cewa kaso biyar daga ciki zai zama mallakin gwamnatin tarayya yayin da take kokarin haɓaka tattalin arziƙi ta hanyar neman sabbin hanyoyin kudin shiga.
A wani labarin kuma 'Da yuwuwar yan takarar APC su yi sulhu yau su fitar da wanda zai gaji Buhari a zaben 2023'
Gwamna kuma ɗan takarar shugaban kasa, Dave Umahi, ya ce wataƙila zuwa anjima su sanar da ɗan takarar da suka yi sulhu.
Jam'iyyar APC na cigaɓa shirye-shiryen zaɓen fitar ɗan takarar shugaban ƙasa, amma Buhari ya buƙaci su yi sulhu tsakanin su.
Asali: Legit.ng