Hotuna: Duk da bai san su ba, Osinbajo ya taimaka wa wasu mutane da suka gwabza hatsari a Abuja

Hotuna: Duk da bai san su ba, Osinbajo ya taimaka wa wasu mutane da suka gwabza hatsari a Abuja

  • Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya taimaka wa wasu mutane da hatsari ya ritsa da su a Abuja
  • Osinbajo na kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama inda zai je Ondo domin ta'aziyya ya ci karo da mummunan hatsarin
  • Ya dakata inda ya taimaka tare da tabbatar da an mika jama'ar asibiti a motar asibiti da ke tawagarsa
  • A halin yanzu ya kira jihar Ondo kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Owo domin jajanta abinda ya faru a majami'ar da 'yan bindiga suka kutsa

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya taimaka wa wasu mutane da hatsari ya ritsa da su a Abuja yayin da ya ke hanyarsa ta zuwa filin sauka da tashin jiragen sama a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Tashin nakiya a coci: Ana ta zaben fidda gwani, Tinubu ya tafi jihar Ondo ziyara

Osinbajo yana kan hanyarsa ne ta zuwa jihar Ondo domin yin ta'aziyyar rayukan da aka rasa a farmakin da miyagu suka kai cocin Owo.

Hotuna: Duk da bai san su ba, Osinbajo ya taimaka wa wasu mutane da suka gwabza hatsari a Abuja
Hotuna: Duk da bai san su ba, Osinbajo ya taimaka wa wasu mutane da suka gwabza hatsari a Abuja.. Hoto daga @akandeoj
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A kan hanyarsa ta zuwa filin sauka da tashin jiragen sama, mataimakin shugaban kasa ya ci karo da wani hatsari da aka tafka a kan titi, ya tsaya domin bada taimako kuma ya tabbatar da an kwashe wadanda lamarin ya shafa an kai su asibiti da motar asibiti da ke tawagarsa.

"Ya karasa inda ya ci gaba da tafiyarsa wanda a halin yanzu yana jihar Ondo inda ya doshi wurin da aka kai farmaki a Owo," Laolu Akande, mai magana da yawun Osinbajo ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Asali: Legit.ng

Online view pixel