Hukuma ta yiwa yan sandan da suka ki karban cin hancin N500,000 ihsani
- Wasu jami'an hukumar yan sandan Najeriya sun samu kyautar kudi bisa jaruntar da suka nuna a bakin aiki
- Hukumar ta bayyana cewa jami'an sun hada da wadanda suka kama yan fashi da makami da wadanda suka kama yan kwaya
- Wadanda suka kama motar kwaya sun ki karbar cin hancin N500,000 da akayi musu tayi don toshiyar baki
Legas - Hukumar Rapid Response Squad (RRS) na yan sandan jihar Legas ta yiwa wasu jami'an hukumarta ihsani bisa jajircewarsu da gaskiya.
Wannan na kunshe cikin jawabin da hukumar ta daura a shafinta na Tuwita ranar Asabar.
Ta baiwa jami'an guda biyar da rundunar 11 kyautar kudi, kambu, da takardar yabo.
Jami'an na cikin wadanda suka damke mota cike da haramtattun kwayoyi kuma suka ki karbar cin hancin N500,000.
Hakazalika sun kwace bindigar AK-47 da wasu bindigogi biyar hannun yan fashi.
Hukumar tace an yi musu wannan karramawa ne saboda jajircewarsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin gabatar da kyaututtukan, Sakataren din-din-din na ofishin shugaban ma'aikatan fada gwamnatin jihar Legas, Olawale Musa, ya jinjina musu bisa gudunmuwar da suke badawa wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Asali: Legit.ng