Hotunan Babura 2,228 da Gwamnatin Legas ta ragargaza yau Juma'a
Legas - Gwamnatin jihar Legas ta fara shirin ragargaza babura Oada kuda 2,228 da aka damke sun saba dokokin da ta santa na haramta aikin Acaba a jihar.
Gwamnatin ta lashi takobin cigaba da damke duk wanda yana tuka babur na haya a kanana hukumomi shida dake jihar da aka haramta aikin.
Kalli hotunan:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yawancin matukan babur na Okada yan ta'adda ne, kwamishanan yan sandan jihar Legas
Kwamishanan yan sandan jihar Legas, Abiodun Alabi, ya bayyana cewa yawancin matasa masu aikin tuka babur a jihar Legas yan ta'adda ne masu aikata laifuka a fadin jihar.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da haramta tukin babur a kananan hukumomi shida a ranar Laraba.
Yayin hira a shirin Sunrise Daily na tashar ChannelsTV ranar Alhamis, Kwamishanan Alabi ya bayyana cewa an kwace lasisin yan babur da yawa bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar.
Yan kasar Nijar, da wasu yan bakin haure ke aikin Okada a Legas, Kwamishanan yan sanda
Kwamishanan yan sandan jihar Legas, Abiodun Alabi, ya bayyana cewa hukumar za tayi fito-na-fito da yan bakin haure dake zuwa jihar aikin babur.
Alabi ya bayyana hakan ranar Juma'a yayin hira da kamfanin dillancin labarai (NAN) a Legas.
Ya ce hukumar na sane da wasu yan bakin haure dake aikin Okada a jihar kuma zasu damke su.
NAN ya ruwaito cewa mafi akasarin masu aiki da babur a Legas ya kasashe mau makwabtaka da Najeriya ne.
Cikinsu akwai yan kasar Nijar, Togo, Kotono da Chadi.
Asali: Legit.ng